A Kauracewa Kallo Fina-Finan Adam A. Zango

Adam a zango

Gobara ce da aka ce ta tashi a masana’antar shirya fina_finan Hausa wato Kannywood tsakanin wasu jarumai biyu da ludayinsu ke kan dawo wato Ali Nuhu da Adam A. Zango bayan cacar baka da sukeyi a shafukansu na sada zumunta.

A makon da ya gabatane dai Adam A. Zango ya fitar da wani hoton bidiyo mai kimanin tsahon mintuna 6 yana kalubalen cewar yafi duk wani bahaushe shahara a fadin kasar Hausa, batun da ya kawo CeCe kuce.

Wasu ma Na ganin kalaman nasa zagi ne a kasuwa bayan da a karo Na biyu Adam A Zango ya kara wallafa wani hoton bidiyo da wasu matasa su biyu suke zagi tare da aibatawa ba tare da sun kama suna ba, amma a Kasan sa Adam Zango ya rubuta babu Wanda ya isa ya zagi mahaifiyarsa ko ya ci mutumcinta ba tare da ya mayar da martani ba, Wanda daga karshe ya liqa sunan Ali Nuhu a nufin shine yake saka yaransa su ci mutuncin Adam Zango.

A daya bangaren kuma Ali Nuhu a shafinsa Na Instagram ya wallafa wani hotonsa yana murmushi ya rubuta ‘Anzo Wajen’, ko da dai bai dauki lokaci ba ya cire hoton.

Adam A Zango dai an San tauraruwarsa ta haska ne dalilin wasu Finafinai da akayi ittifaqin Ali Nuhu ne ya shirya su, amma kuma daga baya Adam Zango ya juya masa baya.

Magoya bayan Ali Nuhu sun dauki matakin tallata kin kallon fina-finan Adam A Zango a qaurace musu don nuna rashin yarda da kalaman batanci da Adam Zango ke yiwa Ali Nuhu.

A yanzu haka a shafin tweeter anyi amfani da #Tag na #BoycottAdamZangofilm, ma’ana a kaurace kallon finafinan Adam Zango don hankalinsa ya dawo jikinsa, tun kafin lokaci ya kure masa.

Usman Solo wani mai sharhine a masana’antar ya wallafa a shafinsa na tweeter cewar  ‘Ali Nuhu shiya dinkawa KANNYWOOD rigar mutunci a idon duniya ya sanya mata, karya ne wani ya tsallako garin Kano yana cimishi mutunci muna kallo… wlh baza mubari ba’

Sannan akwai ra’ayin Bello King Khan da shima ya wallafa a shafinsa na tweeter cewar ‘Akan zagin Ali Nuhu idan Kannywood bata dau mataki ba wlh sai masanaantar tayi danasani, don sai tashafi kowa wallahi.

A yanzu dai maganar kauracewa kallon finafinan Adam Zango shine Wanda ludayinsa me kan dawo wato trending a shafin tweeter a mataki na 6.

AYI SHARSHI

ayi sharhi