Rundunar yansandan Jihar kano ta ja kunnen masu kunnen kashi, dake da shirin zuwa kana nan hukumomin nan guda tara, da za`a sake gudanar da zabe a ranar Asabar mai zuwa da su sake shawara.

Kakakin Rundunar yansandan Jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ta cikin shirin DOKA DA ODA na nan Amunci Radio, inda yace rundunar ba zata lamunci shigar dukka wani bako ba, inda ake gudanar da zaben koda wanne irin dalili gudun tada zaune tsaye, wanda kuma dukka yaki ji, ba zai ki gani ba, dan kuwa rundunar ta shirya tsaf, domin kamu da kuma gurfanar da mutum gaban kuliya manta sabo.

 

Make Comment

Comment