Babu Tabbacin Za’ayi Gasar Olympics A Shekarar 2021

22

Babu tabbacin cewar za agudanar da gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da za ayi a birnin Tokyo na ƙasar Japan a shekara maikamawa wato 2021, wannan magana ta fitone daga bakin shuwagabannin shirya wannan gasa.

Inda shuwagabannin suka ƙara da cewar matuƙar har shekarar 2021 tazo anacikin irin wannan yanayin na cutar Coronavirus kamar yadda akeciki ayanzu to saidai ahakura da fafata gasar zuwa wani lokaci.

Gasar ta Olympics dai anso ayita a shekarar nan ta 2020 amma yadda cutar Covid 19 ta rikirkita duniya hakan yasa aka dakatar dayin gasar gabaɗayanta a wannan shekarar, inda bama iya gasar Olympics ba dukkanin sauran wasubwasannin an dakatar dasu.

A makon daya gabata kwamatin dake shirya gasar ta Olympics ya fitar da maganar cewa an tsayar da ranar 23 ga watan Yuli na shekarar 2021 domin fara gasar inda har akace awaccan ranar yayin bikin buɗe gasar na mintina 15 batare da ‘yan kallo ba.

Comments
Loading...