Hukumar kotunan Jihar kano ta yabawa filin IDON MIKIYA, bisa Namijin kokarin da filin yayi wajan kawo jerin rahotannin irin halin tsaka mai wuyar da kotunan ke ciki na rashin ruwan sha.

A zantwar sa da wakilin mu, Bashir Ahmad Gasau mai magana da yawun kotunan na Jihar Kano BABA JIBO IBRAHIM ya bayyana jin dadinsa a madadin maaikata dama sauran alummar kotunan akan wannan matsala da yace ta zama tarihi ta rashin ruwa a kotu nan, yace wannan nasara ta samu ne sakamakon kwayayatan da filin idon mkiya ya dinga yi watannin baya, da nufin tsikarar mahukuntan da lamarin ya shafa, da fatan su kawo dauki akan matsalar, acewar JIBO hakan kuwa yayi ma`ana gami da nasara dan kuwa kwalliya ta biya kudin sabulu.

Daga karshe yayi kira ga sauran yan jaridu dasu yi koyi da irin wannan nacin bibiyar matsalar al`umma da nufin fatan kawo gyara, da filin Idon mikiya ke yi.

Shirin Idon mikiya dai shiri ne dake bibiyar alamuran yau da kullum da nufin a haskawa mahukunta inda lam`a ta bayyana kuma shirin na zuwar wa mai saurare da karfe 10:00pm na dare sannan a maimaita da karfe 08:30am na safiya.

Wasu mutane dauke da bundigogi sunyi awon gaba da Dagacin karamar hukumar Rogo dake yankin kudancin kano, a wani lamari mai matukar razana zuciya.

Cikakken labarin na tafe ta cikin shirin IDON MIKIYA da karfe 10:00 na dare sannan a maimaita, da karfe 08:30 na safiya.

Direbobin manyan motoci a jihar kano, sun yi kukan cewar yan karota sun matsa musu ta hanyar tilasta musu karbar kudi mafi karnci dubu biyar akan titin mariri dake nan kano.

 

Cikakken labarin na tafe, ta cikin shirin IDON MIKIYA na daren yau litinin 13 01 2020.

Gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir El-rufai ya gudanar da taron majalisar zartarwar Jihar a karo na farko tare da kwamishinonin sa, da nufin tattauna lamurran da zasu ciyar da jihar gaba.

wani bangare na taron zartarwar,

wasu daga kwamishinonin jihar kaduna.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana cewar wasu mutane ne yan kalilan ke gayyato masu satar mutane jihar domin biyan bukatar kansu da kansu.

Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa mazauna garuruwan da ke kan iyakar Najeriya da Nijer ne suka fi yin wannan ta’ada musamman mutanen garin Jibiya.

Ko a ranar Alhamis sai da gwamnan a cikin wani bidiyo wanda yake ta karakaina a shafukan sada zumunta, ba tare da kumbiya-kumbiya ba ya kama sunan mutanen Jibiya inda ya ce su ne ke kara lalata harkar tsaron garunsu da kansu.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wasu jami’an kwastam guda biyu a wani shinge da ke kauyen Dan-bedi a yankin karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina mai iyaka da jamhuriyar Nijer.

Batun hare-hare da sace jama’a dai ya zama ruwan dare a jihar Katisna, inda da wuya rana ta fito ta fadi ba tare da samun wani gari ko kauyen da aka masu satar jama’a suka far wa ba.

Yaron dan shekaru goma yanzu haka na kwance a gadon asibiti, bayan da ilahirin jikinsa ya salube, biyo bayan cusa shi ta karfin tsiya a dakin gasa burodi.

cikakken labarin na tafe ta cikin shirin IDON MIKIYA na yau Alhamis da karfe 10:00 na dare sannan a maimaita da karfe 08:30 na safe zuwa 09:00 na safiya.

Rundunar yansandan kasar nan ta tabbatar da kama wani matashi kuma gawurtaccen mai sayar da makamai ga masu garkuwa da mutane a arewacin kasar nan.

A wani faifan bidiyo da jaridar PRNigeria, ta ce ta samu , mutumin da ake zargin wanda ya yi magana da Hausa a yayin tambayoyin da DSP Hassan Gimba Sule, jami’in ‘yan sanda mai kula da ayyukan rundunar agajin gaggawa ta Special Tactical Squad a jihar Niger ya fitar ya gano wannan matashi na amsa tambayoyi daya bayan daya daga jami`an yansandan.

Mutumin da ake zargin wanda haifaffen jihar Plateau ne ya ce ya kwashe shekaru fiye da uku yana sana’ar sayar da makamai ga yan fashi da sauran yan ta`adda.

Hukumar kula da hadurra ta kasa dake nan kano, ta bayyana mutuwar mutane 12 a kauyen gaya dake nan kano biyo bayan taho mu gamar da wadansu motoci guda biyu kirar GOLF da TOYOTA sukayi a safiyar yau din nan.

Mai Magana da yawun hukumar a nan kano kabiru Ibrahim daura yace, wadanda suka sami raunika tuni suka mika su asibitin gaya domin basu kulawar likitoci.

Kungiyar kwankwasiyya dake rajin kare muradan tsohon gwamnan kano Dr. Rabiu mus kwankwaso sun bayyana aniyar su, ta gurfanar da matashin nan mai suna kabiru muhammad da hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta kama a makon daya gabata da tace shine ya shirya video nan na auren bogi, tsakanin shugaban kasa muhammadu Buhari da kuma wasu ministar kudi zainab Ahmad da kuma ministar bada agaji da taimakon gaggawa sadiya umar farouq.

Sunusi Bature Dawakin tofa dake zaman mai magana da yawun jam`iyyar a nan kano kuma mai magana da yawun dan takarar gwamnan kano a jamiyyar Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewar suna nazarin daawar wannan matashi cewar shi dan kwankwasiyya ne, dan kuwa abun yazo musu da ba zata, kuma matukar suka gano dan kwankwasiyyar ne, ko kuma kalan sharri yake musu zasu gurfanar da shi gaban kotu domin tuhumar sa da bata musu suna.

 

Hukumar tsaron Amurka ta tabbatar da kaiwa wani sansanin sojan Amurkan hari a kasar kenya.

Har wa yau wannan sansanin dake sansanin sojan na MANDA BAY lamarin da hukumar tsaron ke dora alhakin harin akan kungiyar nan ta Al-shabab mai tsats-tsauran ra`ayi.