Masu saurare asslamu alaikum warahmatullah, Abubakar Haruna Galadanchi ne ke farin cikin kasancewa daku a yau ta cikin wani sabon shirin na Idon Mikiya inda zakuji cewa,

 

An gurfanar da wata mata a gaban kotu bisa zargin ta durawa jaririn kishiyarta gishirin lalle a baki.

 

Har yanzu ana cikin wani hali gami da dar dar biyo bayan yadda cutar coronavirus kewa jama`a dauki dai dai.

 

A yi saurare lafiya,

Masu saurare barkan mu da war haka, Abubakar Haruna Galadanchi ke farin cikin kasancewa daku a yau ma ta wani saban shirin na Idon mikiya, ayi saurare lafiya.

Masu saurare Assalamu alaikum, Abubakar Haruna Galadanchi ne ke farin cikin kasancewa daku a wannan rana ta Alhamis cikin wani sabon shirin na IDON MIKIYA, ayi saurare lafiya.

 

 

Masu saurare assalamu alaikum, Abubakar Haruna Galadanchi ne ke farin cikin kasancewa daku a yau, inda zakuji cewa,

 

Rikici akan hula yayi sanadiyyar mutwar wani matashi a nan kano, sai dai yace a yafe masa dan kuwa matar na tuba bata rasa mijin Aure.

 

ku saurara

 

Masu saurare Sannun mu da war haka, Garzali Jibril mai mashi Bebeji sallamar kasancewa daku a yau, inda zakuji cewa,

 

Ku saurara

Ana zargin wani magidanci da karbar Naira dubu 50 daga wadanda ake zargi da yi wa ‘yarsa ciki a jihar Sakkwato.

Wadanda ake zargi da wannan aika aika dai sun hadar da Daraktan Kudi na jihar ta sokoto Ahmad Yahaya Nawawi, da Habibu Abubakar da kuma Karin wani mutum guda da dukkansu ke aiki a Hukumar Tsara Birane bayan da suka yi watanda da yarinyar ‘yar shekaru 14 a duniya mai sayar da ruwan leda, a ofishin daya daga cikinsu abin da ya haifar da shigar cikin da a yanzu ya kai watanni shida.

Sai dai tuni wadanda ake zargi suka amsa laifinsu a ofishin Hukumar dake yaki da masu safarar Mutane ta kasa wato NAPTIP.

Sai dai da yake bawa da bakinsa wuyar sayarwa ne da shi, daya daga cikin wadanda ake tuhumar Nawawi, ya shaida cewa kage ne kawai aka kitsa musu mai cike da siyasa don a bata masa suna a jihar.

 

Hukumar kotunan Jihar kano ta yabawa filin IDON MIKIYA, bisa Namijin kokarin da filin yayi wajan kawo jerin rahotannin irin halin tsaka mai wuyar da kotunan ke ciki na rashin ruwan sha.

A zantwar sa da wakilin mu, Bashir Ahmad Gasau mai magana da yawun kotunan na Jihar Kano BABA JIBO IBRAHIM ya bayyana jin dadinsa a madadin maaikata dama sauran alummar kotunan akan wannan matsala da yace ta zama tarihi ta rashin ruwa a kotu nan, yace wannan nasara ta samu ne sakamakon kwayayatan da filin idon mkiya ya dinga yi watannin baya, da nufin tsikarar mahukuntan da lamarin ya shafa, da fatan su kawo dauki akan matsalar, acewar JIBO hakan kuwa yayi ma`ana gami da nasara dan kuwa kwalliya ta biya kudin sabulu.

Daga karshe yayi kira ga sauran yan jaridu dasu yi koyi da irin wannan nacin bibiyar matsalar al`umma da nufin fatan kawo gyara, da filin Idon mikiya ke yi.

Shirin Idon mikiya dai shiri ne dake bibiyar alamuran yau da kullum da nufin a haskawa mahukunta inda lam`a ta bayyana kuma shirin na zuwar wa mai saurare da karfe 10:00pm na dare sannan a maimaita da karfe 08:30am na safiya.

Wasu mutane dauke da bundigogi sunyi awon gaba da Dagacin karamar hukumar Rogo dake yankin kudancin kano, a wani lamari mai matukar razana zuciya.

Cikakken labarin na tafe ta cikin shirin IDON MIKIYA da karfe 10:00 na dare sannan a maimaita, da karfe 08:30 na safiya.

Direbobin manyan motoci a jihar kano, sun yi kukan cewar yan karota sun matsa musu ta hanyar tilasta musu karbar kudi mafi karnci dubu biyar akan titin mariri dake nan kano.

 

Cikakken labarin na tafe, ta cikin shirin IDON MIKIYA na daren yau litinin 13 01 2020.

Yaron dan shekaru goma yanzu haka na kwance a gadon asibiti, bayan da ilahirin jikinsa ya salube, biyo bayan cusa shi ta karfin tsiya a dakin gasa burodi.

cikakken labarin na tafe ta cikin shirin IDON MIKIYA na yau Alhamis da karfe 10:00 na dare sannan a maimaita da karfe 08:30 na safe zuwa 09:00 na safiya.