Kungiyar kwankwasiyya dake rajin kare muradan tsohon gwamnan kano Dr. Rabiu mus kwankwaso sun bayyana aniyar su, ta gurfanar da matashin nan mai suna kabiru muhammad da hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta kama a makon daya gabata da tace shine ya shirya video nan na auren bogi, tsakanin shugaban kasa muhammadu Buhari da kuma wasu ministar kudi zainab Ahmad da kuma ministar bada agaji da taimakon gaggawa sadiya umar farouq.

Sunusi Bature Dawakin tofa dake zaman mai magana da yawun jam`iyyar a nan kano kuma mai magana da yawun dan takarar gwamnan kano a jamiyyar Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewar suna nazarin daawar wannan matashi cewar shi dan kwankwasiyya ne, dan kuwa abun yazo musu da ba zata, kuma matukar suka gano dan kwankwasiyyar ne, ko kuma kalan sharri yake musu zasu gurfanar da shi gaban kotu domin tuhumar sa da bata musu suna.

 

Hukumar tsaron Amurka ta tabbatar da kaiwa wani sansanin sojan Amurkan hari a kasar kenya.

Har wa yau wannan sansanin dake sansanin sojan na MANDA BAY lamarin da hukumar tsaron ke dora alhakin harin akan kungiyar nan ta Al-shabab mai tsats-tsauran ra`ayi.

Rundunar Yansandan Jihar kano ta tabbatar da kama wata matar Aure a karamar Hukumar Rano dake kudancin Jihar kano data jefa kishiyarta a rijiya mai dauke da jariri dan watanni a duniya.

Rundunar ta kuma bayyana cewar ta samu nasarar cafke kishiyar ne, bayan da Zaratan jamianta suka bi bayan matar lokacin da zakara ya bata saa, lamarin da ita kuwa kishiyar bayan cirota rai yayi halinsa.

Cikakken labarin na tafe ta cikin shirin IDON MIKIYA  ranar litinin da karfe 10:00 na dare sannan a maimaita da karfe 08:30 na safiya.

Kwamishinan yansanda na Jihar kano, Habu Sani Amadu ya ja kunnen sababin yansandan da aka yiwa karin girma dasu tabbata sun baiwa marada kunya.

Wannan na Zuwa ne alokacin da kwamishiann ya jagorancin karin girma ga wasu daga Jami`an rundunar daga mukamin CSP zuwa mataimakin kwamishinan yansanda su 7, a inda mataimakan kwamishinan yansanda su 6 suka zama mukaddasan kwamishinan yansandan su 6.

Daga bisani mukaddashin kwamishinan yansandan na jihar kano mai kula da ayyuka na musamman, DCP BALARABE SULE ya kara da cewar wadannan suka dace da samun girman su tabbata sun rike ayyukansu da kyau domin gudun jawowa rundunar abun fada.

 

Mummunar Gobarar ta tashi ne, alokacin da mai junan biyun ke barci ita da sauran yayanta uku, lamarin da tayi sanadiyyar mutuwar mai cikin da yayanta baki daya, a wani lamari mai matukar tada Hankali.

Cikakken labarin na tafe ta cikin shirin IDON MIKIYA na daren yau Alhamis da karfe 10:00 na dare sannan maimaici na tafe da safiya da karfe 08:30 zuwa 09:00.

Wasu magoya bayan kasar Iran masu zanga-zanga a Iraki sun fara kafa tantuna da niyyar zaman dirshen a gaban ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Bagadaza.

Masu zanga-zangar sun bayyana cewa ba za su daina zanga-zangar ba, kuma ba za su bar gaban ofishin jakadancin ba har sai sojojin Amurka sun fice daga Iraki.

A ranar Talata ne wasu masu zanga-zanga suka cinna wuta a wasu sassan ofishin jakadancin Amurkar da ke Bagdaza biyo bayan wani hari ta sama da Amurka ta kai wa kungiyar mayakan sa-kai da Iran ke goya wa baya a Iraki.

Kimanin mayaka 25 ne suka mutu lokacin da Amurkan ta kai hare-haren a sansanin mayakan masu alaka da kungiyar Kataib Hezbollah a Iraki da Syria ranar Lahadi.

Sai dai shugaban Amurka Trump ya bayyana cewar kasar ta Iraqi zata sha ammaki, a wani lamari daya kira barazana ce kai tsaye domin kare muradan Amurka.

HOSPITAL

Wani buncike da filin idon mikiya ya gudanar ya gano yadda wani Asibiti a jihar nan, ke daukar likitoci aiki da baki, kana da sun ga dama zasu kore ka ne da baki, ba tare da wata girmamawa ba a matsayinka na likita.

A dakace mu…

DADIYATA

Hukumar tsaro ta afrin kaya wato DSS ta karyata labarin da ta ce wasu jaridun kasar nan sun wallafa cewa tana tsare da mutum kusan 50 kuma take azabtar da su.

Mai magana da yawun Hukumar Dr. peter Afunanya ne ya bayyana haka, inda yace don wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da Dadiyata, ba zai zama dalilin da za a ce jami’an hukumar ba ne.

Sanarwar ta ce babu dalilin da zai sa DSS ta musanta wadanda ta kama ko take tsare da su idan har kuma ta kaddamar da samame har ta kai ga kama wani dan kuwa aiki take bisa ka`ida da kuma tanade tanaden kunidn tsarin mulkin tarayyar kasar nan.

 

 

Hukumar Hisbar dai ta bayyana damke wannan Dansanda a lokacin da ta kai samame wani otal, inda ta tarar da wannan dansanda a daki tare da yan mata uku a wani yanayi mai munin gaske.

 

Cikakken labarin na tafe ta cikin shirin IDON MIKIYA na daren yau Talata 31-12-2019 da karfe 10:00 zuwa 10:30 na dare sannan a maimaita da karfe 08:30 zuwa 09:00 na safiya.