A wani bunciken kwa-kwaf da filin IDON MIKIYA ya gudanar ya gano yadda asibitin sha ka tafi na unguwar tsamiya babba dake yankin karamar hukumar Gezawa a nan kano, ke kwana a bude han-hai duk da irin kayayyakin maganin da kayan aiki na dubban Nairori da gwamnati ta samar domin amfanin marasa lafiya.

Har ila yau, batun zuwan maaikatan wannan Asibiti bakin aiki kuwa abun baa cewa komai dan kuwa 11:00 na rana kanyi ba tare da anga keyar likita ba, ko kuma wani ma`aikacin lafiya ba koda guda daya da yazo domin sauraren marasa lafiya wadanda a hannu guda kuma, filin idon mikiya yayi tozali da cunkoson marasa lafiya  sunyi layi suna jiran likita.

zamu ci gaba….

A wani lamari mai kama gaggawa, dattawan karamar hukumar Bagwai sun bayyana cewar, daga yanzu dole ne, dukka saurayi da budurwa ko kuma Bazawari da Bazawarar da zasu yi aure sai an musu gwajin jini domin gudun fadawa matsala da yada cutuka.

Wannan na zuwa ne, a dai dai lokacin da sakamakon gwajin lafiya na gama gari ke bayyana dumbin masu cutuka a tsakanin samari da zawarawan yankin.

Cikakken labarin na tafe ta cikin shirin IDON MIKIYA a gobe litinin da karfe 10:00 na dare sannan a maimaita da karfe 08:30 na safiya.

A dai dai lokacin da muke gab da ban kwana da shekarar 2019 al`amura da dama sun faru, wanda kuma kai tsaye muka kawo muku ta cikin shirin IDON MIKIYA da yake zuwar muku kullum da karfe 10:00 na dare sannan a maimaita da karfe 08:30 na safiya kowacce rana, ba shakka ba zasu lissafu ba.

Filin Idon mikiya na sauraren shawarwari ko kuma gyararraki daga gareku koma sanar damu faruwar wadansu al`amura da kuke gani a sabuwar shekarar nan shirin IDON MIKIYA ya mai da hankali a kansu, ko kuma sake bibiyarsu domin fatan an baiwa mai hakki hakkinsa.

Har ila yau, tare da dakon ra`ayoyinku dangane da shirin baki daya dama yadda kuke ganin zamu inganta wadansu ayyukan shiri akan lambobin nan da aka saba 08134982159 ko kuma 08106475938 da kuma 08064947417.

Sai munji daga gare ku.

A dai dai lokacin da muke gab da bankwana da shekarar 2019 al`amura da dama sun faru, wanda kuma kai tsaye muka kawo muku ta cikin shirin IDON MIKIYA da yake zuwar muku kullum da karfe 10:00 na dare sannan a maimaita da karfe 08:30 na safiya kowacce rana, ba shakka ba zasu lissafu ba.