Yau Litinin 10/02/2020CE wanda yayi daidai da 15/06/1441AH.

Ga cikakkun labaran

Majalisar wakilai ta hurowa Hafsun Sojoji wuta ta ce su yi murabus ko a tsige su ta dole.

‘Yansanda sun kama wadanda suka kai wa Sarkin Potiskum hari a hanyar Kaduna zuwa Zaria kwanakin baya.

Hukumar EFCC ta bankado cewa tsohon gwamnan jihar Abia, Theodore Orji duk wata sai ya saci Naira milyan 500 a lokacin yana mulki.

Sarkin Musulmi ya ce babu shakka Talakawa na cikin bala’i a Najeriya.

Rundunar ‘yansanda ta ce ta gano masu goyon bayan kungiyar ta’addancin na Al’ansaru.

Sojojin Amurka 2 da kuma daya na Afghanistan ne aka kashe a wani hari a gabashin kasar Afghanistan.

Coronavirus: ‘Yan Ingila biyar sun kamu da cutar a kasar Faransa.

An fara sufuri a filin tashi da saukar jiragen saman Libiya.

Npfl:MFM ta kawo karshen wasanni 13 da Kano Pillars tayi batare da tayi nasara ba, inda ta caskara Pillars daci 3 da 1.

Seria A: Inter Milan ta lashe AC Milan 4:2 awasan hamayya da suka fafata

LaLiga: Barcelona ta ci Real Betis 3:2 a wasan da suka buga jiya.

Ligue 1: PSG ta ci Lyon 4:2 a wasan da suka buga jiya.

Yau 04/02/2020CE wanda yayi daidai da 09/06/1441AH.

Ga cikakkun labaran:

Tsohon Shugaban kasa, Jonathan ya ce karfin sojoji ba zai samar da tsaro a Najeriya ba.

Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da tsarin ba da bizar Najeriya na 2020.

Mutane 376,631 suka nemi guraben aiki na 220 a hukumar ICPC.

Matasan APC sun sha alwashin tona asirin ‘yan majalisan da ke neman hambarar da Buhari.

‘Yansanda sun yi nasarar kama manyan masu garkuwa da mutane su 4 a hanyar Abuja-Lokoja.

Rundunar ‘yansanda a jihar Kaduna ta bayar da umurnin a dawo da binciken jaka a kasuwanni da makarantu da wuraren bauta.

Jigo a jam’iyyar PDP wato Doyin Okupe, yana so a canza wa jam’iyyar suna saboda ta samu karbuwa.

Mafi karancin albashi: Kungiyar kwadago a jihar Neja ta umarci ma’aikatan gwamnati su fara yajin aikin dindindin tunda anki a fara biyansu adadin kudin da akace za a biya na 30000

Hukumar kwastam ta kama makudan kudade da suka kai kimanin $8m a filin jirgin sama na jahar Lagos.

An yi watsi da bukatar kwashe ‘yan Najeriya daga daga kasar China saboda cutar Coronavirus.

Iran ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa saboda yi wa CIA aikin leken asiri.

Wata Kotu ta ba da izinin kama Jacob Zuma na Afirka ta Kudu.

Kotu ta samu Maryam Sanda da laifin ‘kashe mijinta’

Wata babbar kotu a Abuja ta samu Maryam Sanda da laifin ‘kashe mijinta’.

Sashin Hausa na BBC ya rawaito a yau Litinin ne dai kotun ta yanke hukunci a kan shari’ar Maryam Sanda, matar da ake zargi da kashe mijinta Bilyaminu Bello a 2017.

Da farko dai Maryam ta musanta zargin inda ta ce zamewa mijin nata ya yi inda ya fadi a kan kuttun shisha wanda ya yi ajalinsa.

An gurfanar da ita a gaban kotu tare da dan uwanta da mahaifiyarta da ‘yar aikinta da ake zargi da lalata shedun da ke nuna ta aikata laifin da ake zargin ta a kai.

Bayan sauraron bangarorin da ke shari’ar a ranar 25 ga watan Nuwamban 2019, alkali Yusuf Halilu ya sanya ranar 27 ga watan Janairun 2020 a matsayin ranar yanke hukunci.

Yau 22/05/1441AH wanda yayi daidai da 18/01/2020CE

Kiris yarage asha bikin wata baturiya datazo daga kasar Amurka da saurayin dazata aura dan asalin jahar Kano wanda suka hadu a dandalin sada zumunta.

Gawurtaccen mai garkuwa da mutane, Buju Bazamfare ya mika kansa ga hukuma a jihar Nasarawa.

Jagorar IPOB, Nnamdi Kanu zai shigo Najeriya jana’izar iyayensa wata mai zuwa.

Shugaban sojojin sama, AM Saddique ya ce an sayi jiragen yaki don kawar da Boko Haram.

Badakalar satar N200m: jami’an EFCC sun kama akawun majalisa, matarsa da yaransa 2 a jihar Benue.

Tanko Yakasai ya ce dole ne Inyamurai su hada kai da mutanen Arewa muddin suna son su mulki Najeriya.

Shugaban sojoji, Buratai ya amincewa sojoji amfani da sigari da sauran abubuwan more rayuwa a fagen fama.

Jam’iyyar PDP za ta shirya zanga-zanga kan hukuncin da kotun koli ta yanke na gwamnan jihar Imo.

Sudan ta kudu ta gaza kulla yarjejeniyar sulhu da ‘yan tawaye.

lsraila ta kame wasu ‘yan kasar Finlan su 5 a yayin da suke kan hanyarsu ta shiga Zirrin Gaza daga yankin Israila.

Indiya ta samu nasarar harba tauraron dan adam na GSAT-30 zuwa duniyar sama.

Masu horas wa sama da 50 ne suka nuna sha awarsu ta horas da kungiyoyin kwallon kafa na kasar nan kama daga ‘yan kasa da shekara 17 zuwa Super Eagles.

Harry Maguire ya zama sabon Kaftin din kungiyar Manchester United.

Babbar Jam’iyyar hamayya a Najeriya PDP ta ce ta yi mamakin hukuncin da kotun koli ta yanke kan zaben gwamnan jihar Imo

A ranar Talata ne kotun koli ta kwace kujerar gwamna daga Emeka Ihedioha na Jam’iyyar PDP ta baiwa Hope Uzodinma na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sanarwar da kakakin jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan ya fitar bayan zartar da hukuncin ta ce, PDP ta kasa fahimtar dalilan da kotun koli ta yi dogaro da su na yanke hukuncin.

PDP ta kasa fahimtar yadda za a ce dan takarar da ya zo na hudu a zaben gwamna na 9 ga Maris da kuri’a 96,458 ace ya doke dan takarar PDP da ya samu yawan kuri’u 276,404

Sai dai kuma jam’iyyar APC ta bayyana farin cikinta da hukuncin Kotun kolin da ta bayyana dan takararta Hope Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Imo.

Gwamnatin tarayya ta sanar da haramta kungiyar tsaro ta Amotekun, da wasu jihohin shiyyar kudu suka samar.

Kafa rundunr tsaron ya janyo ce-ce-ku-ce inda wasu ke ganin za ta iya zama barazana ga kasar a nan gaba.

Mai taimaka wa Ministan Shari’ar kasar nan a fannin yada labarai Dakta Umar Jibrilu Gwandu ya shaida wa manema labarai cewa batun samar da tsaro da makami hakki ne da ya rataya kan gwamnatin Tarayya kadai.

Ya jaddada cewa kirkirar kungiyar wani laifi ne da ya sabawa doka, domin an yi tanadin jami’an tsaron soji da na ‘yan sanda da na ruwa da kuma sojin sama, wadanda su ne ke da alhakin tabbatar da tsaro a dukkanin sassan Najeriya.

Gwamnatin Jihar Yobe Ta Kafa Kwamitin Tattauna Batun Aiwatar Da Albashi Mafi Karanci

Matakin na zuwa ne a cikin wata takardar amincewa da kafa kwamitin wadda ta kunshi amincewar Gwamna Mai Mala Buni wajen nada wadanda zasu jagoranci kwamitin

Kamar yadda wasikar ta bayyana, kwamiti ya kunshi mutum goma a karkashin mukaddashin shugaban ma’aikatan jihar ta Yobe, Mohammed Nura hadi da sakatarorin din-din-din a sashen mulki da manyan ayyuka, da ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki da sauransu.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC) reshen jihar Yobe, tare da na shugaban hadaddiyar kungiyar shiga-tsakani ta ma’aikatan gwamnati.

Haka kuma, wannan matakin zai kwantar da hankalin ma’aikatan jihar bisa yadda suka dade suna jiran makamanciyar irin wannan rana, ganin an dauki dogon lokaci gwamnatin jihar ba ta ce uffan ba dangane da lamarin, ballantana kuma kungiyar ma’aikatan kwadago ta kasa reshen jihar Yobe.

Kotun Koli Ta Saka Ranar Yanke Hukuncin Zaben Gwamna A Kano.

 

Kotun Koli a tarayyar kasa ta bayyana ranar Litinin 20 ga watan Janairun 2020 zata yanke hukuncin karshe kan shari’ar da akeyi tsakanin Abdullahi Ganduje na Jam’iyyar APC da kuma Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar PDP da kuma Hukumar Zabe INEC.

Dan Takarar PDP, Abba Kabir Yusuf ne ke kalubalantar zaben da hukumar zabe ta ayyana Abdullahi Ganduje a matsayin wanda yayi nasara.

Kotun Kolin ta sanar da ranar da zata yanke hukuncin karshe, bayan lauyoyin bangarorin su tafka muhawara tsakani.

 

Karanta: KOTUN KOLI A NAJERIYA ZATA BAYYANA SAHIHANCI KUJERAR GANDUJE A RANAR LITININ

KOTUN KOLI TA DAGE ZAMANTA KAN SHARI’AR GWAMNONI

 

Kotun Koli ta Dage zamanta kan shari’ar Gwamnoni a Najeriya, zuwa ranar Talata 14 ga watan Janairu na 2020.

Wannan ya biyo bayan rashin lafiya da daya daga cikin mutane 7 masu gudanar shari’ar kamar yadda Alkalin Alkalai Justice Muhammad Tanko ya Bayyana.

Tun da farko dai a bayyana harabar kotun ta dinke da mutane, wanda hakan ya kawo tsaiko da gudanar da al’amura yadda ya kamata a zauren Kotun.

Cikin Jihohin da Dage yanke hukuncin ya shafa, akwai Kano, Sokoto, Benue, Pilato, da kuma Imo.

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid wato Zinedine Yazid Zidane yaci gaba da kafa tarihi a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.

Yaci gaba da kafa tarihinne bayan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lashe gasar Spanish Supercopa adaren Lahadi ahannun kungiyar kwallon kafa ta Athletico Madrid.

Inda wannan nasara da Real Madrid tayi ya nuna cewa Zidane ya jagoranci Real Madrid wasannin karshe guda 9 kuma dukkaninsu yayi nasara.

Hakan tasa ya kafa tarihi na lashe kofuna guda 10 a kungiyar kwallon kafan idan aka hada da kofin gasar Laliga daya lashe.

Gidan Rediyon Aminchi yasami tattaunawa da Zahrah Cr7 mai goyon bayan Real Madrid dake jahar Kano dangane da nasarar da Madrid ta samu inda tace “ai daman mu Madrid duniya ce, kuma jami’ar kwallon kafa, ina mai tabbatar da cewa duk kungiyar kwallon kafan datace zataja da Real Madrid wato Jami’ar Kwallon kafa to carry over ce akanta domin bama rasa wasan karshe kaga sunanmu gidan nasara”