Fasaha ce hanyar magance yaduwar coronavirus
Nasan mai karatu zaiyi mamakin wannan furucin ‘Fasaha ce hanyar magance yaduwar coronavirus”. To amma ba abin mamaki bane duba da yadda al’amuran duniya suke sauyawa a kowanne lokaci ta hanyar amfani da kimiyya da fasaha.

Kusan a halin yanzu babu wani abu da ake tattaunawa kansa duniya baki daya da ya wuce cutar Coronavirus. Saboda cutace mai yaduwa ta hanyoyi da dama, wadda saboda irin illolin dake tattare da ita, kasancewar kafafen sadarwa musamman masu yada labarai har kullum su na bayyana irin ta’adin da wannan cuta take yi kasashen da suka kamu da ita.

Takai ta kawo a wasu kasashen an hana cudanya ga jama’a domin dakile yaduwar ta a tsakanin a’umma. Kuma a halin yanzu ana ta kokarin shawo kanta a duniya baki daya. Bazan cika ku da surutu akan irin illar wannan cuta ba saboda labarinta ya zamo ruwan dare. Zan mayar da hankali ne akan yadda ake amfani da fasaha domin gudanar da al’amuran rayuwa na yau da kullum ba tare da anyi cudanya ba a tsakanin jama’a wanda hakan shi ne matakin da kasashen duniya suka dauka a matsayin kariya musamman kasashen da akafi samun masu cutar.

Tuntuni fasaha ta samar da tsarin gudanar da aikin ofis daga gida (Work from home), ko karatu daga gida (Remote Learning har ma da siye da siyarwa daga gida ta shafin intanet. Haka zalika a halin yanzu wannan al’amari ya kara samun karbuwa, duba da yadda cudanya ko mu’amala ta zahiri tsakanin al’umma ya zamo barazana ga lafiyar su a duniya musamman a kashen da cutar ta fi yin illa.

Labarai sun bayyana cewa kasar Sa’udiya ma ta dauki matakin rufe manya da kananan makarantu, domin dakile yaduwar wannan cita a tsakanin. Haka ma kasashe da yawa sun dauki wannan tsari na rage cudanya tsakanin al’uamma domin asamr da kariya. To abin dubawa anan shine; Matakan tsaro ga na’urori da sadarwa tsakanin na’urorin domin haki da cutar na’urar kanta har ma da masu kutse.

Saboda kada ya zamo ana maganin kaba kuma kai yana kumbura. Wato kada ya zamo ana maganin yaduwar cutar coronavirus a tsakanin al’aumma, ba tare da an dauki kwararan matakan kariya ga na’urori da sadarwar su dangane da ta su cutar Virus da masu kutse ba. Dole ne a samar da matakan tsaro wajan yin karatu, aiki da sauran al’amura da ake iya gudanarwa ta hanayar fasahar sadarwa ta intanet.

Fasahar tsaro ta VPN a tsarin sadarwa tsakanin na’urori da intanet
mataki tsaro na VPN

Wannan dalili ya sanya aka kirkiro da tsarin amfani matakin tsaro ta sadarwa tsakanin na’urori da intanet (VPN). Wanda a halin yanzu shi ne tsarin da wadancan kasa she da suke amfani da fasaha wajan gudanar da aikace-aikacen yau da kullum. Saidai wani hanzari ba gudu ba, wannan hanya ko fasaha ta VPN tana da muhimmanci, kuma yanda kayu a fahimci yadda take, kamar haka;

Tana rage saurin intanet saboda yawan killace-killace dake cikin tsarin ta

Samarda wannan fasahar ta VPN ta kashin kai akwai tsadar gaske.
Kuma yana da kyau a sani cewa VPN ba intanet ba ne. Amma da matakin tsaro ne na sadarwa tsakanin na’urori da intanet.
Tanada saukin amfani ga kowa
Idan har ana amfani da intanet irin na kyauta kamar (Pulic Wi fi), ya zamo dole ayi amfani da VPN domin tsaro.
Insha Allahu zanyi cikakken rubutu nan gaba akan VPN domin a sami fahimtar tsarin sosai.

matsalolin wayar salula

Wani bincike da likitocin kwakwalwa suka gudanar ya ce kusan kashi daya bisa uku na matasa sun shaku da wayoyin zamani har ma abin ke neman zame musu kamar ba za su iya rayuwa sai da waya.

Binciken da kwalejin Kings a birnin London ta yi ya ce mutane na shiga yanayin damuwa a duk lokacin da aka ce ba su tare da wayoyinsu.

Rahoton ya ce matasa ba sa iya takaita lokacin da suke shafewa suna dannar waya.

Binciken ya kuma ce irin wannan shakuwa da wayoyin zamani na iya shafar lafiyar kwakwalwar mutum.

Shi dai binciken, wanda aka wallafa a mujallar BMC Psychiatry, ya yi nazari kan wasu bincike har 41 da aka yi kan matasa 42,000 game da matsalar amfani da wayoyin zamani.

Binciken ya gano cewa kashi 23 cikin dari na matasan, waya ta zame musu kamar abin da ba za su iya rayuwa ba sai da ita – irin halin da suke shiga idan ba sa iya amfani da wayarsu da kuma rashin iya kayyade lokacin da suke shafewa akan wayoyin har ta kai ga hakan na zama hadari ga wasu harkokinsu.

Irin wannan dabi’a ta shakuwa da waya ana iya danganta ta da sauran matsaloli, kamar yadda binciken ya bayyana, kamar gajiya, da damuwa da rashin bacci da kuma rashin yin kokari a makaranta.

Daya daga cikin wadanda suka wallafa rahoton, Nicola Kalk daga cibiyar kula da lafiyar kwakwalwa a kwalejin Kings da ke birnin London, ya ce, “wayoyin zamani sun samu wajen zama kuma akwai bukatar a fahimci irin matsalolin da ke tattare da amfani da wayoyin.”

A cewar Dr Kalk, ”ba mu sani ba ko wayar zamanin ce ta ke da shiga ran mai ita ko kuma manhajojin da mutane suke amfani da su.

“Duk da haka, akwai bukatar a wayar wa da mutane kai game da yadda yara da matasa ke amfani da wayoyin zamani da kuma bukatar iyaye su san iya lokacin da ‘ya’yansu suke shafewa akan wayoyinsu.”

Ita ma Samantha Sohn, ta ce shakuwa da waya na “iya shafar lafiyar kwakwalwa da kuma harkokin yau da kullum, akwai bukatar a zurfafa bincike kan matsalolin da ke tattare da yin amfani da wayoyin zamani”.

Sai dai Amy Orben, wata malama a sashen kimiyyar kwakwalwa a jami’ar Cambridge, ta ja hankali game da tunanin cewa akwai wata alaka tsakanin yawan amfani da wayoyin zamani da kuma matsalolin damuwa’.’

A cewarta, a baya, an nuna cewa illar yin amfani da wayoyin zamani ba wai daga wayoyin ba ne kadai, yanayin mutum ma kan iya yanke yawan lokacin da mutum zai shafe akan waya”.

Source: Link

shafin google zai dakatar da tallan siyasa

Kamfanin Google ya sanar da kudirinsa na dakatar da duk wasu tallace-tallace da suka shafi yakin neman zaben siyasa.

Sabon tsarin zai hana masu talla yin amfani da siyasa da bayanan masu zabe wajen aike sakonsu ga wasu mutane da aka kebe.

A gaba kuma, masu zaben za su kasance an takaita su ga yin amfani da shekaru da jinsi da kuma wajen da mutum yake, yayin yanke hukunci kan wanda za su aike wa sakon.

Sabon tsarin zai fara ne a Burtaniya cikin mako guda gabanin babban zaben da za a gudanar ranar 20 ga watan Disamba, wanda daga bisani kuma za a fara amfani da tsarin a fadin duniya.

Google ya kara da cewa zai dauki mataki kan tallace-tallacen da ake tsara su domin yaudarar jama’a, inda suka raba gari da Facebook ta nan.

Mark Zuckerberg ya ce shafin sada zumuntarsa ba zai dinga bin diddigin tallace-tallacen ‘yan siyasa da na yakin neman zabe ba.

A hannu guda kuma, Twitter ya ce zai hana tallace-tallacen da suka shafi siyasa.

Source: Link

Akwai yiwuwar cewa matasan da ke kashe sama da awa uku a rana a kan shafukan sada zumunta ba za su yi bacci ba sai bayan karfe sha daya na dare kuma za su iya farkawa cikin daren, in ji wani bincike da aka gudanar a Birtaniya.

Wannan na shafar matashi daya cikin uku- inda matashi daya cikin biyar ke kashe sa’o’i biyar ko fiye a manhajoji kamar su Instagram da Whatsapp da Facebook kullum, a cewar binciken.

Masu bincike a jamai’ar Glasgow sun ce akwai yiwuwar cewa matasa ‘yan shekara 13 zuwa 15 na jan kafa wajen kwanciya bacci saboda suna amfani da wayoyinsu.

Likitocin lafiyar kwakwalwa sun ce a daina amfani da waya awa daya kafin a kwanta bacci.

Sai dai binciken da aka gudanar na matasa 12,000 ya gano cewa hana matasa amfani da waya zai iya zama babbar matsala saboda lokaci ne na cin gashin kansu, lokaci mai muhimmanci da suke zumunci da abokansu.

Binciken ya kara tabbatar da wani hasashe na cewa lokacin da matasa ke batawa a kan shafukan sada zumunta na rage lokutan da suke dauka suna bacci- kuma rashin bacci na tasiri a kan lafiyar kwakwalwa da kokarin makaranta.

Sa’o’i nawa matasa ke kashewa a shafukan sada zumunta?

Sa’o’i a rana Kashin matasa maza Kashin matasa mata Kashin duka matasa
Kasa da sa’a daya 43.8 22.8 33.7
Tsakanin sa’a daya da sa’o’i uku 32.1 31.1 31.6
Daga sa’a uku zuwa biyar 10.4 17.7 13.9
Sama da sa’a biyar 13.7 28.4 20.8

‘Kar a yi ba su’

Dakta Holly Scott ta bangaren ilimin halayyar dan Adam na Jami’ar Glasgow, ta ce binciken bai iya tabbatar da cewa yawan amfani da shafukan sada zumunta na jawo rashin isasshen bacci ba, amma da alama yana takara sosai da bacci.

“Matasa na iya kwanciya amma idonsu biyu saboda basu shirya yin baccin ba kuma suna fargabar cewa idan suka yi bacci suka fita daga shafukan za a yi ba su”

Dakta Max Davie ta Kwalejin lafiyar yara ta ce isasshen bacci mai inganci na da muhimmanci ga yara da matasa.

“Muna bayara da shawarar cewa matasa sun daina amfani da wayoyinsu a kalla awa daya kafin su kwanta bacci saboda kwakwalwarsu ta samu ta huta.

“Rashin bacci na da mummunan tasiri ga lafiyar matasa da dangantakarsu da sauran ‘yan uwansu da abokansu da kuma kokarinsu a makaranta.”

 

Tushen Labari

Ba kamfanonin waya ne kadai ke cinye muku data ba

Hukumar ta ce ba ko yaushe bane kamfanonin waya ke da laifin karar da data ba gaira ba dalili, idan masu amfani da intanet a waya suka ga data a wayarsu na saurin karewa.

NCC ta kirki layin 622 na kira kyauta don a kai koke a duk lokacin da wani kamfanin sadarwa ya zuke wa wani data ba kan ka’ida ba.

Shugaban Hukumar, Farfesa Umar Danbatta ya bayyana haka ne a wani rahoto da ya gabatar ga Ministan Sadarwa Dakta Isa Ali Pantami da kuma wasu jami’a na ma’aikatar.

Danbatta ya bayyana cewa habakar kimiyya ce ta janyo ake kirkirar manhajoji daban-daban, wadanda za a ga cewa wadannan manhajojin na cikin waya na sabunta kansu ba tare da ainahin mai wayar ya sani ba, sakamakon haka sai data ta yi ta tafiya ba tare da mutum ya sani ba.

Ya kuma bayyana cewa idan mutum na shiga shafukan sada zumunta, ana yawan tallace-tallace ta hanyar amfani da bidiyo, ya ce a wani lokacin bidiyon yakan fara ne ba tare da mutum ya sani ba, wanda hakan wata hanya ce da ke cinye data.

A taron tattaunawar, hukumar ta NCC ta ce za ta kara bita ko kuma waiwayar batun farashin siyan data da kuma ingancinta.

Sai dai Ministan Sadarwa Isa Pantami ya bayyana cewa hukumar NCC na aiki tukuru, amma su yi kokari wajen wayar da kan al’umma a kafafen yada labarai ta hanyar amfani da harsuna daban-daban domin jama’a su gane gaskiyar wannan lamari.

Tushen Labari