namadobi

Sashin labarai na Amunci Radio muke gabatar muku da BITAR LABARAN MAKO.

Shiri ne da yake bitar manyan labarun da suka wakana ta cikin makon da muke bankwana da shi.

Hakazalika a shirin zai zo da tattaunawa tare da masanin al`amuran yau da kullum Dr. Kabiru Sufi, inda zaa tattauna akan makomar shugaban Amurka Donald Trump da kuma batun karin kudin wutar lantarki.

Karibullah Abdulhamid Namadobi da Jam`arsa na tafe ta cikin shirin da karfe 06:30 na yammacin kowacce lahadi.

 

Muna dakon sakonnin ku

Hukumar Yaki da Masu Yiwa Tattalin Arziki Kasa Ta’annati EFCC ta daskarar da asusun Banki na ajiya mallakar tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya Shehu Sani.

Babban Mashawarci ga Sanata Shehu Sani, Malqm Sulaiman Ahmad ne ya tabbatarwa da Manema Labarai Lamarin a ranar Lahadi
A senior special adviser to Senator Shehu Sani, kuma Hukumar ta tursasawa Shehu Sani bayyana kadarorin da ya mallaka.

Malam Ahmad ya kalubalanci EFCC da nuna rashin kwarewar aiki, inda ya nuna mamakin yadda Hukumar ta yi watsi da kama Wanda ke zargin Shehu Sani, duk da ya bayyana kokarin bayar da cin hanci.

Tun a ranar 31 ga Watan Disambar bara Hukumar ke tuhumar Shehu Sani akan badakalar kudade tsakaninsa da wani Dan Kasuwa mai kamfanin ASD, wato Alhaji Sani Dauda, da kudi Dala $24,000.

Ayau za a fafata wasan karshe na gasar Super Cup tsakanin manyan kungiyoyin kwallon kafa guda biyu kuma wadanda suka fito daga birni daya wato birnin Madrid na kasar Andalos.

Wannan wasa za ayishi tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da Athletico Madrid.

Inda za a fafata wannan wasa a kasar Saudiyya da misalin karfe 7:00 na dare agogon Najeriya.

Acikin shekaru 6 dai kungiyoyin kwallon kafan guda biyu sun fafata wasannin karshe sau 3 inda suka fafata guda biyu agasar zakarun nahiyar turai a 2014 da 2016 inda Real Madrid ta lashe Athletico Madrid aduk wasanni biyun.

Sai kuma a gasar Toyota inda Athletico Madrid ta lashe Real Madrid.

Shin ko yau waye zai zamo zakara?

Sashen wasanni na Aminchi Radio ya tattauna ya tattauna da Aliyu Safyan Alhasan wanda magoyin bayan Real Madrid ne dake jahar Kano kuma daya daga cikin ma’aikatan Aminchi Radio na sashen siyasa inda yace “mu Real Madrid duniya ne kuma ni naso ace Barcelona ne suka fito wasan karshen nan aga yadda zamu ragargazasu domin sai sunfi saukin cinyewa, amma duk da haka suma Athletico Madrid insha Allah zamu lashesu daci 2 da 1 domin wasan kariya zasuyi wato defending”

KOTUN KOLI A NAJERIYA ZATA BAYYANA SAHIHANCI KUJERAR GANDUJE A RANAR LITININ

 

Kotun Koli a tarayyar Najeriya zata yanke hukuncin karar da Dan Takarar Gwamna na Jam’iyyar PDP a Kano Engr. Abba Kabir Yusuf a Ranar Litinin, da yake kalubalantar sahihancin zaben da Hukumar Zabe mai Zaman Kanta INEC ta ayyana Abdullahi Umar Ganduje na jamiyyar APC a matsayin Wanda ya lashe zaben Gwamna a Kano na 2019.

 

Engr Abba Kabir Yusuf ne tun a farko ya garzaya Kotun Karbar Korafin Zabe, inda kuma Hajiya Halima Shamaki da ta jagoranci shari’ar ta tabbatar da sahihinacin zaben da akayiwa Ganduje.

 

Haka ma a Kotun Daukaka Kara Ganduje ya sake samun nasara akan Engr Abba Kabir Yusuf.

Yau Alhamis 9/01/2020CE – wanda yayi daidai da 13/05/1441AH.

Ga cikakkun labaran:

Rundunar sojoji sun kai wa ‘yan bindiga hari a sansaninsu da ke Jibia na jihar Katsina.

Fasto Mathew Kukah ya ce bambanci gwamnatin Buhari da Boko Haram shi ne tashin bam.

Gwamna ganduje ya kalubalanci dattijan Kano a kan kirkirar sabbin masarautu a gaban kotu. Ya ce ba za su rushe burin mutane miliyan 20 ba na jihar.

Tubabbun ‘yan bindigan Zamfara sun yi taro a daji don tattaunawa kan yarjejeniyar da suka yi da Gwamna Matawalle.

Jami’ar Bayero da ke Kano ta karrama wata Baturiya da ta kwashe shekaru 50 tana koyar da harshen Hausa.

Rikicin cikin gida: Jam’iyyar PDP ta dare gida biyu a jihar Kano.

Kotu ta sanar da ranar 27 ga watan Janairu don yanke hukunci kan sabbin masarautun Kano.

Mutum 12 sun mutu a wani hadarin motoci da ya afku a kauyen Tsaida da ke karamar hukumar Gaya a jahar Kano.

Shugaba Trump na Amurka ya ce babu sojar Amurka da aka kashe a harin da Iran ta kai Iraki.

Iran ta ce ba za ta mika wa Amurka bakin akwatin Jirgin Ukraine da ya yi hatsari ba.

Ajiya aka fafata wasannin mako na 13 na gasar ajin Premier ta kasar nan a filayen wasanni daban daban ciki harda wasan da Kano Pillars ta tashi kunnen doki.

Super Cup: Real Madrid ta ci Valencia 3:1 a wasan jiya.

Yau 22/12/2019CE – daidai da 23/04/1441AH.

Gwamna Ganduje na jihar Kano ya yi wa manyan sakatarorin gwamnatinsa canjin wuraren aiki.

Wani Sifetan ‘yan sanda, John Markus, ya kashe wani abokin aikinsa sannan daga baya ya kashe kansa a Abuja.

Gwamna Zulum na jihar Borno ya bayar da umurnin soma aikin koda kyauta a jihar.

Mabiya darikar Tijjaniya sun kai ziyarar nuna goyon bayansu ga Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Masu garkuwa da suka sace hakimi a Birnin Gwari sun bukaci a biya su Naira milyan 30.

An yanke wa wani malamin jami’an da ya yi batanci ga Annabi Muhammad SAW a shafinsa na sada zumunta hukuncin kisa a Pakistan.

Kasar Rasha ta yi wa Amurka raddi game da takunkumin tattalin arziki.

Mutane 18 ne suka rasa rayukansu sakamakon wata rigima da ta barke a wani gidan yari dake Honduras inda kuma wasu 16 suka jikkata.

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool tazamo zakara agasar zakarun nahiyoyi da aka kammala a jiya bayan sunsha dakyar ahannun kungiyar kwallon kafa ta Flamengo.

Dan wasan Gabon, Pierre-Emerick Aubameyang yana son barin Arsenal.

Ayau Lahadi za a fafata wasannin mako na 8 na gasar ajin Premier ta kasar nan.

Saidai wasan da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars zata fafata da Nasarawa United agarin lafiya an dage wasan sakamakon gwamnatin jahar Nasarawa zatayi taro a filin.

Ga jerin wasannin daza a buga a yau:

Adamawa United da SunshineStars

Kwara United da Heartland

Plateau United da Ifeanyi Uba

Jigawa Golden Stars da Warri Wolves

Lobi Stars da Abia Warriors

Dakkada F/C da Enyimba

Rivers United da Katsina United

Yau 12 ga watan Disamba, 2019 wanda yayi daidai da 15 ga watan Rabiu Thani Hijira ta 1441.

Ga Cikakkun Labaran:

Sanatoci sun bukaci adinga biyan masu zaman kashe wando albashi tunda gwamnati ta gaza samar da ayyukan yi.

Gwamnatin jihar Kano za ta kafa dokar hana aurar da ‘yan mata kafin su kammala sakandare.

Sanata Shehu ya ce yanan a siyasance Kuma zai kara fitowa takara a 2023.

Fatima Abdullahi, ‘yar uwar Maina uwa daya, uba daya ta nesanta kanta da shi a yayin ba da shaida a gaban kotu.

Gwamnatin jihar Jigawa za ta kashe Naira miliyan 60 wajen gina dakunan ‘ba haya’.

Femi Fani Kayode ya gargadi shugaba Buhari kan yin katsalandan kan shari’ar zaben gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde.

Jami’an tsaro na FBI a Amurka sun kama jirgin wani attajirin dan Najeriya kan zarginsa da damfara da safarar miyagun kwayoyi.

Majalisar Dinkin Duniya ta aike da tireloli 32 dauke da kayan taimako zuwa yankin Idlib na arewacin Siriya.

A wani gidan gona dake yankin Suffolk na Ingila an bayyana bullar murar tsuntsaye.

Dada bangaren wasanni kuwa zakuji cewar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta bayyana cewar har yanzu hukumar kwallon kafa ta kasar nan bata biyasu kudinsu ba na gasar Aiteo Cup da suka lashe wato naira miliyan 25.

Ajiya aka kammala wasannin rukuni na gasar cin kofin zakarun nahiyar turai.

Ayau za a fafata wasannin gasar ajin kwararru ta nahiyar turai.

Daga Suraj Na’iya Kududdufawa

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars sun lallasa Akwa Starlet har gida a kwantan wasansu na mako na biyu na gasar ajin Premier ta kasar nan.

Yau shine karon farko da Kano Pillars tasami nasara tunda aka fara gasar ta bana biyo bayan rashin nasarori da kungiyar tayi fama dashi inda kujerar masu horas da kungiyar take rawa ganin cewar zasu iya rasa aikinsu.

Yanzu dai Pillars nada maki 6 daga cikin wasanni 6 dasuka buga a gasar.

Akarshen makon daya gabata ne dai mai horas da kungiyar kwallon kafan ta Kano Pillars ya bayyana cewar yana ganin cewar Kano Pillars ne zasu lashe gasar ta bana.

Yau shine karon farko da Akwa Starlet tayi rashin nasara inda yanzu suna da maki 11 daga waaanni 6 da suka fafata.

Daga Suraj Na’iya Kududdufawa.

Kungiyar kwallon kafa ta Jigawa Golden Stars ta caskara Ifenyi Uba awasan mako na 6 na gasar ajin Premier ta kasar nan.

Jigawan ta lallasasu daci 2 da 1 afilin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata wanda awannan fili jigawan take buga wasannin ta na gida.

Ayanzu dai Jigawa suna matsayi na 15 da maki sakamakon nasarar da suka samu a yammacin yau.

Itakuma Ifenyi Uba duk da ansami nasara akansu suna matsayi na 9 da maki 8.