Ba kamfanonin waya ne kadai ke cinye muku data ba

Hukumar ta ce ba ko yaushe bane kamfanonin waya ke da laifin karar da data ba gaira ba dalili, idan masu amfani da intanet a waya suka ga data a wayarsu na saurin karewa.

NCC ta kirki layin 622 na kira kyauta don a kai koke a duk lokacin da wani kamfanin sadarwa ya zuke wa wani data ba kan ka’ida ba.

Shugaban Hukumar, Farfesa Umar Danbatta ya bayyana haka ne a wani rahoto da ya gabatar ga Ministan Sadarwa Dakta Isa Ali Pantami da kuma wasu jami’a na ma’aikatar.

Danbatta ya bayyana cewa habakar kimiyya ce ta janyo ake kirkirar manhajoji daban-daban, wadanda za a ga cewa wadannan manhajojin na cikin waya na sabunta kansu ba tare da ainahin mai wayar ya sani ba, sakamakon haka sai data ta yi ta tafiya ba tare da mutum ya sani ba.

Ya kuma bayyana cewa idan mutum na shiga shafukan sada zumunta, ana yawan tallace-tallace ta hanyar amfani da bidiyo, ya ce a wani lokacin bidiyon yakan fara ne ba tare da mutum ya sani ba, wanda hakan wata hanya ce da ke cinye data.

A taron tattaunawar, hukumar ta NCC ta ce za ta kara bita ko kuma waiwayar batun farashin siyan data da kuma ingancinta.

Sai dai Ministan Sadarwa Isa Pantami ya bayyana cewa hukumar NCC na aiki tukuru, amma su yi kokari wajen wayar da kan al’umma a kafafen yada labarai ta hanyar amfani da harsuna daban-daban domin jama’a su gane gaskiyar wannan lamari.

Tushen Labari

Adam a zango

Gobara ce da aka ce ta tashi a masana’antar shirya fina_finan Hausa wato Kannywood tsakanin wasu jarumai biyu da ludayinsu ke kan dawo wato Ali Nuhu da Adam A. Zango bayan cacar baka da sukeyi a shafukansu na sada zumunta.

A makon da ya gabatane dai Adam A. Zango ya fitar da wani hoton bidiyo mai kimanin tsahon mintuna 6 yana kalubalen cewar yafi duk wani bahaushe shahara a fadin kasar Hausa, batun da ya kawo CeCe kuce.

Wasu ma Na ganin kalaman nasa zagi ne a kasuwa bayan da a karo Na biyu Adam A Zango ya kara wallafa wani hoton bidiyo da wasu matasa su biyu suke zagi tare da aibatawa ba tare da sun kama suna ba, amma a Kasan sa Adam Zango ya rubuta babu Wanda ya isa ya zagi mahaifiyarsa ko ya ci mutumcinta ba tare da ya mayar da martani ba, Wanda daga karshe ya liqa sunan Ali Nuhu a nufin shine yake saka yaransa su ci mutuncin Adam Zango.

A daya bangaren kuma Ali Nuhu a shafinsa Na Instagram ya wallafa wani hotonsa yana murmushi ya rubuta ‘Anzo Wajen’, ko da dai bai dauki lokaci ba ya cire hoton.

Adam A Zango dai an San tauraruwarsa ta haska ne dalilin wasu Finafinai da akayi ittifaqin Ali Nuhu ne ya shirya su, amma kuma daga baya Adam Zango ya juya masa baya.

Magoya bayan Ali Nuhu sun dauki matakin tallata kin kallon fina-finan Adam A Zango a qaurace musu don nuna rashin yarda da kalaman batanci da Adam Zango ke yiwa Ali Nuhu.

A yanzu haka a shafin tweeter anyi amfani da #Tag na #BoycottAdamZangofilm, ma’ana a kaurace kallon finafinan Adam Zango don hankalinsa ya dawo jikinsa, tun kafin lokaci ya kure masa.

Usman Solo wani mai sharhine a masana’antar ya wallafa a shafinsa na tweeter cewar  ‘Ali Nuhu shiya dinkawa KANNYWOOD rigar mutunci a idon duniya ya sanya mata, karya ne wani ya tsallako garin Kano yana cimishi mutunci muna kallo… wlh baza mubari ba’

Sannan akwai ra’ayin Bello King Khan da shima ya wallafa a shafinsa na tweeter cewar ‘Akan zagin Ali Nuhu idan Kannywood bata dau mataki ba wlh sai masanaantar tayi danasani, don sai tashafi kowa wallahi.

A yanzu dai maganar kauracewa kallon finafinan Adam Zango shine Wanda ludayinsa me kan dawo wato trending a shafin tweeter a mataki na 6.

Hukumar zabe ta kasa

Hukumar Zabe ta Kasa ta ayyana ranar laraba 3 ga watan Afrilu zata baiwa Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Shaidar dake nuna an zabe shi matsayin Gwamnan Kano a karo na biyu.

Gwamna Ganduje wanda ya sami tazarar kuri’u tsakaninsa da ‘Dan Takarar Jam’iyyar PDP Injiniya Abba Kabir Yusuf bayan zaben da tun a farko aka ayyana bai kammalu ba, yanzu haka dai a wata takarda da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta mikawa jam’iyyar APC reshen jihar Kano, tace ta gamsu da zaben da akayiwa Ganduje a ranar 23 ga watan maris din da ya gabata.

Sai dai kuma Jam’iyyar PDP tace zaben cike gurbin da akayi a wasu kananan hukumomi musamman karamar hukumar Nassarawa a Mazabar Gama, an samu rigingimu da kuma zargin hada kai wajen hana magoya bayan PDP kada kuri’unsu, a don haka ma ta yanke hukuncin kalubalantar zaben a gaban kotun da aka tanada don karbar korafe korafen zabe.

A ranar Laraba ne dai za’ayi bikin mika shaidar ga Gwamna Ganduje da kuma Mambobin Majalisar dokoki na jihar Kano da aka zaba.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa an kashe wata ‘yar Najeriya a Saudiyya bayan kama ta da laifin safarar miyagun kwayoyi.

An kashe matar ne tare da wasu maza biyu ‘yan Pakistan da wani guda daya dan Yemen a Makka, birni mafi tsarki a kasar ranar Litinin.

A shekarar nan kawai an kashe mutane 53, a cewar AFP.

Saudiyya dai ta tirje duk da matsin lambar da take fuskanta daga kungiyoyin kare hakkin dan Adam, na ta kawar da hukuncin kisa.

Kasar ta sha yankewa mutane da dama hukuncin kisa, ciki har da masu fafutukar kare hakkin dan Adam da ‘yan ta’adda.

A bara ne ma kasar ta yi yunkurin yanke wa wata mai fafutukar kare hakkin mata Israa al-Ghomgham wacce aka yi amannar cewa ita ce ‘yar kasar Saudiyya ta farko da take fuskantar hukuncin kisa saboda ayyukanta na kare hakkin mata.

aminci radio

Al`amarin dai ya faru ne a kauyen Urami dake karamar Hukumar Bakori ta Jihar katsina, Bayanda marigayi Ango Aminu aka daura Auransa da sahibarsa watanni tara da suka gabata.

Tun da farko dai sai da wata yar`uwar babar sa ta nuna tirjyarta akan wannan aure inda tace nata dan daban ne zai auri wannan matashiya ba wai shi Aminu ba, lamarin da mahaifin Amaryar ya nuna rashin Amuncewa akan haka, saboda acewar mahaifin Aminu marigayi shine ya fara nuna yana san yar tasa, dan haka ba zai yi magana Biyu ba.

Daga nan ne dai wancan lamari da alama bai yiwa ita yaruwar Ango mai rasuwa  dadi ba, inda tace tunda aka hana danta Auren wannan yarinya zaai auren ta gani, lamarinda acewar kanwar babar Aminu Ango marigayi tun daga ranar da aka daura Auren ya shiga dakin Amaryar tasa bai kara samun lafiya ba, saboda tsananin ciwan ciki.

Tace babban abun dake basu tsoro shine  ciwan ciki daya dinga turnuke Aminu inda daga bisani sai aman guntattakin likkafani, naman kawunan tsuntsaye harma da Hakora da dan kunne, wanda a haka dai harta kaiga ranar daya koma ga Allah ta kasance dashi, watanni tara bayan Daura masa Aure.

Ga dai karin bayani daga wakilin filin IDAN MIKIYA Abdurrahman yusuf Dunbulun da yayi tattaki har kauyen na Urami dake karamar Hukumar Bakori a jihar ta katsina, inda ya nemi tattaunawa da Mahaifiyar marigayi Aminu, sai dai kasancewar tana cikin rudanin mutuwa bata iya cewa komai ba, sai dai ga abunda kanwar babar tasa wadda kuma duk abun daya faru, a idanuwansu ne ta bayyana masa.

Babban fatan mu dai Allah kaji kan wannan Ango, mu kuma ka karemu daga shaidanun mutane ameen  .