Babbar Jam’iyyar hamayya a Najeriya PDP ta ce ta yi mamakin hukuncin da kotun koli ta yanke kan zaben gwamnan jihar Imo

A ranar Talata ne kotun koli ta kwace kujerar gwamna daga Emeka Ihedioha na Jam’iyyar PDP ta baiwa Hope Uzodinma na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sanarwar da kakakin jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan ya fitar bayan zartar da hukuncin ta ce, PDP ta kasa fahimtar dalilan da kotun koli ta yi dogaro da su na yanke hukuncin.

PDP ta kasa fahimtar yadda za a ce dan takarar da ya zo na hudu a zaben gwamna na 9 ga Maris da kuri’a 96,458 ace ya doke dan takarar PDP da ya samu yawan kuri’u 276,404

Sai dai kuma jam’iyyar APC ta bayyana farin cikinta da hukuncin Kotun kolin da ta bayyana dan takararta Hope Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Imo.

Kotun Koli Ta Saka Ranar Yanke Hukuncin Zaben Gwamna A Kano.

 

Kotun Koli a tarayyar kasa ta bayyana ranar Litinin 20 ga watan Janairun 2020 zata yanke hukuncin karshe kan shari’ar da akeyi tsakanin Abdullahi Ganduje na Jam’iyyar APC da kuma Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar PDP da kuma Hukumar Zabe INEC.

Dan Takarar PDP, Abba Kabir Yusuf ne ke kalubalantar zaben da hukumar zabe ta ayyana Abdullahi Ganduje a matsayin wanda yayi nasara.

Kotun Kolin ta sanar da ranar da zata yanke hukuncin karshe, bayan lauyoyin bangarorin su tafka muhawara tsakani.

 

Karanta: KOTUN KOLI A NAJERIYA ZATA BAYYANA SAHIHANCI KUJERAR GANDUJE A RANAR LITININ

KOTUN KOLI TA DAGE ZAMANTA KAN SHARI’AR GWAMNONI

 

Kotun Koli ta Dage zamanta kan shari’ar Gwamnoni a Najeriya, zuwa ranar Talata 14 ga watan Janairu na 2020.

Wannan ya biyo bayan rashin lafiya da daya daga cikin mutane 7 masu gudanar shari’ar kamar yadda Alkalin Alkalai Justice Muhammad Tanko ya Bayyana.

Tun da farko dai a bayyana harabar kotun ta dinke da mutane, wanda hakan ya kawo tsaiko da gudanar da al’amura yadda ya kamata a zauren Kotun.

Cikin Jihohin da Dage yanke hukuncin ya shafa, akwai Kano, Sokoto, Benue, Pilato, da kuma Imo.

Hukumar Yaki da Masu Yiwa Tattalin Arziki Kasa Ta’annati EFCC ta daskarar da asusun Banki na ajiya mallakar tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya Shehu Sani.

Babban Mashawarci ga Sanata Shehu Sani, Malqm Sulaiman Ahmad ne ya tabbatarwa da Manema Labarai Lamarin a ranar Lahadi
A senior special adviser to Senator Shehu Sani, kuma Hukumar ta tursasawa Shehu Sani bayyana kadarorin da ya mallaka.

Malam Ahmad ya kalubalanci EFCC da nuna rashin kwarewar aiki, inda ya nuna mamakin yadda Hukumar ta yi watsi da kama Wanda ke zargin Shehu Sani, duk da ya bayyana kokarin bayar da cin hanci.

Tun a ranar 31 ga Watan Disambar bara Hukumar ke tuhumar Shehu Sani akan badakalar kudade tsakaninsa da wani Dan Kasuwa mai kamfanin ASD, wato Alhaji Sani Dauda, da kudi Dala $24,000.

KOTUN KOLI A NAJERIYA ZATA BAYYANA SAHIHANCI KUJERAR GANDUJE A RANAR LITININ

 

Kotun Koli a tarayyar Najeriya zata yanke hukuncin karar da Dan Takarar Gwamna na Jam’iyyar PDP a Kano Engr. Abba Kabir Yusuf a Ranar Litinin, da yake kalubalantar sahihancin zaben da Hukumar Zabe mai Zaman Kanta INEC ta ayyana Abdullahi Umar Ganduje na jamiyyar APC a matsayin Wanda ya lashe zaben Gwamna a Kano na 2019.

 

Engr Abba Kabir Yusuf ne tun a farko ya garzaya Kotun Karbar Korafin Zabe, inda kuma Hajiya Halima Shamaki da ta jagoranci shari’ar ta tabbatar da sahihinacin zaben da akayiwa Ganduje.

 

Haka ma a Kotun Daukaka Kara Ganduje ya sake samun nasara akan Engr Abba Kabir Yusuf.