Dole samari da zawarawa suyi gwajin jini kafin Aure ko rai ya baci-Dattawan Bagwai

14

A wani lamari mai kama gaggawa, dattawan karamar hukumar Bagwai sun bayyana cewar, daga yanzu dole ne, dukka saurayi da budurwa ko kuma Bazawari da Bazawarar da zasu yi aure sai an musu gwajin jini domin gudun fadawa matsala da yada cutuka.

Wannan na zuwa ne, a dai dai lokacin da sakamakon gwajin lafiya na gama gari ke bayyana dumbin masu cutuka a tsakanin samari da zawarawan yankin.

Cikakken labarin na tafe ta cikin shirin IDON MIKIYA a gobe litinin da karfe 10:00 na dare sannan a maimaita da karfe 08:30 na safiya.

Comments
Loading...