Duniyar Fasaha

January 15, 2018

Duniyar Fasaha, shiri ne, da  ya kunshi tattaunawa da kuma bayyani akan abinda ya shafi Na’urori da ake amfani dasu a ko’ina domin saukaka aikace-aikacen yau da kullum, tsahon minti 30 a kowacce ranar Laraba da misalin karfe 12:00 na rana, ana kuma maimaita shirin a duk ranar Litinin da misalin karfe 6:30 zuwa 7:00na safe.

A cikin shirin akanyi duba ga yadda wannan fasaha ta zamani ta samar da cigaba ta fuskoki daban-daban na rayuwa a wannan duniyar tamu. Kuma wannan shiri ana gabatar dashi ne cikin harshen hausa domin a samar da kyakykyawar fahimta ga al’uma musamman matasa da dalibai dake nazari a fannin kimiyya da fasahar zamani da kuma sauran fannonin nazari daban-daban.

A cikin shirin mukan amsa tambayoyin masu sauraro domin warware matsala ko karin haske dangane da na’urori da ake ta’ammali dasu wajen gudanar da al’amuran yau da kullum; a gidaje, makarantu, kasuwanni, ofisoshi, masana’antu, dakunan bincike da sauran wuraren da amfani da na’urori kan saukaka mu’amala. Wanda wadannan na’urori suna da ruwa da tsaki wajen sauya tsare-tsaren tafiyar da al’amuran rayuwar yau da kullum a doro irin na zamani.

Bugu da kari a cikin shirin muna karbar shawarwari daga masana ko gayyatar su domin yi fashin baki dangane da wani al’amarin da ya shiga duhu musamman wajen sarrafawa ko mu’amalada na’ura. Sannan wannan shiri yanada shafi a dandanlin zumunta na facebook (Duniyar Fasaha – Aminci Radio 103.9FM) da kuma lambar waya (08054381702) domin neman karin bayani, tambaya ko bada gudummawa a cikin shirin.

A cikin shirin duniyar fasaha, muna amfani da gwargwadon bayani cikin harshen hausa domin bayyana wasu sassa na na’urori wasu kuma muna ambatar sunayen su na asali kasnacewar mu’amalar yau da kullum ta sa an saba dasu kamar yadda sukazo.

Muna matukar godiya a bisa goyon baya, kwarin gwiwa da kuma addu’o’in da ma’abota wannan shiri da ma masu sauraron wannan tasha ta Aminci Radio wadda keyi domin cigaban al’umma, muna godiya Allah ya kara dankon zumunci.

 

Aminci Radio domin cigaban al’umma