Gwamnatin Jihar Yobe Ta Kafa Kwamitin Tattauna Batun Aiwatar Da Albashi Mafi Karanci

Matakin na zuwa ne a cikin wata takardar amincewa da kafa kwamitin wadda ta kunshi amincewar Gwamna Mai Mala Buni wajen nada wadanda zasu jagoranci kwamitin

Kamar yadda wasikar ta bayyana, kwamiti ya kunshi mutum goma a karkashin mukaddashin shugaban ma’aikatan jihar ta Yobe, Mohammed Nura hadi da sakatarorin din-din-din a sashen mulki da manyan ayyuka, da ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki da sauransu.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC) reshen jihar Yobe, tare da na shugaban hadaddiyar kungiyar shiga-tsakani ta ma’aikatan gwamnati.

Haka kuma, wannan matakin zai kwantar da hankalin ma’aikatan jihar bisa yadda suka dade suna jiran makamanciyar irin wannan rana, ganin an dauki dogon lokaci gwamnatin jihar ba ta ce uffan ba dangane da lamarin, ballantana kuma kungiyar ma’aikatan kwadago ta kasa reshen jihar Yobe.

Make Comment

Comment