HADARIN MOTA YA LAKUME RAYUKAN MUTANE 12 A KANO

14

Hukumar kula da hadurra ta kasa dake nan kano, ta bayyana mutuwar mutane 12 a kauyen gaya dake nan kano biyo bayan taho mu gamar da wadansu motoci guda biyu kirar GOLF da TOYOTA sukayi a safiyar yau din nan.

Mai Magana da yawun hukumar a nan kano kabiru Ibrahim daura yace, wadanda suka sami raunika tuni suka mika su asibitin gaya domin basu kulawar likitoci.

Comments
Loading...