Hukumar Zabe ta Kasa ta Bayyana Ranar Laraba zata mikawa Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da ‘Yan Majalisar Jiha Shaidar Zabar su da akayi

Hukumar zabe ta kasa

Hukumar Zabe ta Kasa ta ayyana ranar laraba 3 ga watan Afrilu zata baiwa Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Shaidar dake nuna an zabe shi matsayin Gwamnan Kano a karo na biyu.

Gwamna Ganduje wanda ya sami tazarar kuri’u tsakaninsa da ‘Dan Takarar Jam’iyyar PDP Injiniya Abba Kabir Yusuf bayan zaben da tun a farko aka ayyana bai kammalu ba, yanzu haka dai a wata takarda da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta mikawa jam’iyyar APC reshen jihar Kano, tace ta gamsu da zaben da akayiwa Ganduje a ranar 23 ga watan maris din da ya gabata.

Sai dai kuma Jam’iyyar PDP tace zaben cike gurbin da akayi a wasu kananan hukumomi musamman karamar hukumar Nassarawa a Mazabar Gama, an samu rigingimu da kuma zargin hada kai wajen hana magoya bayan PDP kada kuri’unsu, a don haka ma ta yanke hukuncin kalubalantar zaben a gaban kotun da aka tanada don karbar korafe korafen zabe.

A ranar Laraba ne dai za’ayi bikin mika shaidar ga Gwamna Ganduje da kuma Mambobin Majalisar dokoki na jihar Kano da aka zaba.

AYI SHARSHI

ayi sharhi