IRAN ZATA SHA MAMAKI-DONALD TRUMP

11

Wasu magoya bayan kasar Iran masu zanga-zanga a Iraki sun fara kafa tantuna da niyyar zaman dirshen a gaban ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Bagadaza.

Masu zanga-zangar sun bayyana cewa ba za su daina zanga-zangar ba, kuma ba za su bar gaban ofishin jakadancin ba har sai sojojin Amurka sun fice daga Iraki.

A ranar Talata ne wasu masu zanga-zanga suka cinna wuta a wasu sassan ofishin jakadancin Amurkar da ke Bagdaza biyo bayan wani hari ta sama da Amurka ta kai wa kungiyar mayakan sa-kai da Iran ke goya wa baya a Iraki.

Kimanin mayaka 25 ne suka mutu lokacin da Amurkan ta kai hare-haren a sansanin mayakan masu alaka da kungiyar Kataib Hezbollah a Iraki da Syria ranar Lahadi.

Sai dai shugaban Amurka Trump ya bayyana cewar kasar ta Iraqi zata sha ammaki, a wani lamari daya kira barazana ce kai tsaye domin kare muradan Amurka.

Comments
Loading...