Kano Pillara Bazasu Buga Wasansuba Akarahen Mako

109

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars bazasu fafata wasansu na mako na biyu ba na gasar ajin Premier ta kasar nan.

Kano Pillars din dai zatai tattaki zuwa jahar Akwa Ibom ne domin buga wasa da kungiyar kwallon kafa ta Akwa Starlets.

Hukumar shirya gasar ta a jin Premier ta kasar nan ce ta bayyana hakan na cewa andage wannan wasa amma nan gaba za a sanar da ranar da za a fafata wannan wasa na mako na biyu.

Wasan makon farko dai da Kano Pillars din ta fafata da kungiyar kwallon kafa ta Rivers United antashi wasa babu ci wato kunnen doki kenan.

Hakama dai itama kungiyar kwallon kafa ta Akwa United an dage wasansu da Abia Warriors amma wannan wasan za a fafata shi a ranar Alhamis idan Allah ya kaimu.

Comments
Loading...