Daga Suraj Na’iya Kududdufawa

Tub bayan zuwan tsohin mai horas da kungiyoyin kwallon kafan Lorca Deportiva da Almeria da Valencia da Spartak Mascow da Sevilla harma da Paris Saint Germain wato Unai Emery Etxegoien ya karbi ragamar horas da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal abubuwa suka fara dadi a kungiyar kwallon kafan bayan yin wasu wasanni masu yawa batare da ansami nasara akan Arsenal ba.

Amma daga bisani abubuwa suka tabarbare na rashin nasara inda da wuya Arsenal sujera wasanni 3 ajere sunayin nasara.

Hasali ma dai a ‘yan kwanakinnan Arsenal sun jera wasanni 7 batare da sunyi nasara ba inda ko a jiya agasar Europa league ta nahiyar turai an lallasa Arsenal har gida daci 2 da 1.

Hasali ma akwai alamu da rade-radin cewar wasu ‘yan wasan basa jiyuwa da Emery a zamantakewarsu musamman Ozil da Xhaka da sauransu.

Hakama magoya bayan Arsenal na duniya baki daya cewa suke ya kamata a sallami Unai Emery domin koma baya yake jawowa Arsenal har wasu na cewa gara tsohon mai horas wa Arsen Wenger.

Ta tabbata ayau Arsenal sun kori Unai Emery bayan ya kwashe shekara 1 da rabi wato watanni 18 a kungiyar.

Shin kowa Arsenal zasu kawo domin maye gurbin Unai Emery?

Make Comment

Comment