Kwankwaso Bashi da Hujja akan zargin Shugaban Kasa Muhammad Buhari shine ya bada Umarnin Cire Sarki Muhammad Sanusi II – Muhammad Garba

12

Kwankwaso Bashi da Hujja akan zargin Shugaban Kasa Muhammad Buhari shine ya bada Umarnin Cire Sarki Muhammad Sanusi II – Muhammad Garba

Kwamishinan Yada Labarai na Gwamnatin Kano Muhammad Garba, ya mayar da martani ga tsohon Gwamnan Kano Injiya Rabiu Musa Kwankwaso, kan zargin umarni Gwamna Ganduje ya karba daga Shugaban Kasa Muhammad Buhari don sauke Sarkin Kano Muhammad Sanusi daga sarkin kano.

Cikin wata tattaunawa ta musamman da wakilinmu Aliyu Sufyan Alhassan, Kwamishinan yace “Babu wata gamsasshiyar hujja da Kwankwaso zai gabatar da ke nuna Umarni aka karba don daukar matakin tsige Muhammad Sanusi II daga Sarkin Kano”. Inji Muhammad Garba

Dangane da Zargin tursasa rike Sarkin Kano da lauyoyinsa sukayi Kwamishinan yace ” Suna da damar da doka ta basu, amma kada su manta, tarihi ya nuna duk sarkin da yayi murabus, ko aka sauke shi, dole ne a killaceshi a wani waje, domin bashi tsaro na musamman”.

Gwamnatin Kano ta sauke Sarki Sanusi II, tare da maye gurbinsa da ‘Dan Marigayi Sarkin Kano Ado Bayero wato Aminu Ado Bayero a matsayin sabon ‘Sarkin Cikin Gari’.

Comments
Loading...