Labaran Safiyar Alhamis

6

Yau Alhamis 9/01/2020CE – wanda yayi daidai da 13/05/1441AH.

Ga cikakkun labaran:

Rundunar sojoji sun kai wa ‘yan bindiga hari a sansaninsu da ke Jibia na jihar Katsina.

Fasto Mathew Kukah ya ce bambanci gwamnatin Buhari da Boko Haram shi ne tashin bam.

Gwamna ganduje ya kalubalanci dattijan Kano a kan kirkirar sabbin masarautu a gaban kotu. Ya ce ba za su rushe burin mutane miliyan 20 ba na jihar.

Tubabbun ‘yan bindigan Zamfara sun yi taro a daji don tattaunawa kan yarjejeniyar da suka yi da Gwamna Matawalle.

Jami’ar Bayero da ke Kano ta karrama wata Baturiya da ta kwashe shekaru 50 tana koyar da harshen Hausa.

Rikicin cikin gida: Jam’iyyar PDP ta dare gida biyu a jihar Kano.

Kotu ta sanar da ranar 27 ga watan Janairu don yanke hukunci kan sabbin masarautun Kano.

Mutum 12 sun mutu a wani hadarin motoci da ya afku a kauyen Tsaida da ke karamar hukumar Gaya a jahar Kano.

Shugaba Trump na Amurka ya ce babu sojar Amurka da aka kashe a harin da Iran ta kai Iraki.

Iran ta ce ba za ta mika wa Amurka bakin akwatin Jirgin Ukraine da ya yi hatsari ba.

Ajiya aka fafata wasannin mako na 13 na gasar ajin Premier ta kasar nan a filayen wasanni daban daban ciki harda wasan da Kano Pillars ta tashi kunnen doki.

Super Cup: Real Madrid ta ci Valencia 3:1 a wasan jiya.

Comments
Loading...