Yau 22/12/2019CE – daidai da 23/04/1441AH.

Gwamna Ganduje na jihar Kano ya yi wa manyan sakatarorin gwamnatinsa canjin wuraren aiki.

Wani Sifetan ‘yan sanda, John Markus, ya kashe wani abokin aikinsa sannan daga baya ya kashe kansa a Abuja.

Gwamna Zulum na jihar Borno ya bayar da umurnin soma aikin koda kyauta a jihar.

Mabiya darikar Tijjaniya sun kai ziyarar nuna goyon bayansu ga Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Masu garkuwa da suka sace hakimi a Birnin Gwari sun bukaci a biya su Naira milyan 30.

An yanke wa wani malamin jami’an da ya yi batanci ga Annabi Muhammad SAW a shafinsa na sada zumunta hukuncin kisa a Pakistan.

Kasar Rasha ta yi wa Amurka raddi game da takunkumin tattalin arziki.

Mutane 18 ne suka rasa rayukansu sakamakon wata rigima da ta barke a wani gidan yari dake Honduras inda kuma wasu 16 suka jikkata.

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool tazamo zakara agasar zakarun nahiyoyi da aka kammala a jiya bayan sunsha dakyar ahannun kungiyar kwallon kafa ta Flamengo.

Dan wasan Gabon, Pierre-Emerick Aubameyang yana son barin Arsenal.

Make Comment

Comment