Labaran Yammacin Talata Da Ɗumi-ɗuminsu

259

Yau Talata 7/12/1441AH wanda yayi daidai da 28/7/2020.

An gano wasu lakcarori na ma’aikanan tarayya dana jaha dakecin moriyar aikin N-Power afaɗin tarayyar ƙasar nan.

Ayammacin yau shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gana da wasu daga cikin gwannonin APC.

Ministan yaɗa labarai wato Lai Muhammad ya ce an ƙawto Dala bilyan 800 a hannun barayin gwamnatin ƙasar nan.

Wata kotu ta bayar da umurnin cafke tsohon magatakardan majalisar tarayya wato Sani Omolori.

Kotun ɗaukaka ƙara da ke babban birnin tarraya Abuja ta yi fatali da ƙarar da Dino Melaye ya ɗaukaka na ƙalubalantar nasarar da Smart Adeyemi yayi.

Hukumar DSS ta ce ta gano wani shiri da akeyi akan ƙasar Najeriya domin a tarwatsata gabaɗaya.

Tsohon ɗan takarar gwamnan jahar Kano a jam’iyyar PDP wato Abba gida-gida ya gurfanar da Ganduje a gaban kotu dangane da sayar da katafaren Otel ɗin Daula dake jahar Kano.

Gwamna jahar Bauchi Bala Muhammad yace Dogara ya koma APC don yana da hannu a badaƙalar hukumar NDDC.

Kwamitin bincike na AfDB ya wanke Akinwumi Adesina, daga zarge-zargen cin hanci da nuna bangaranci da akeyimasa.

Kamfanin Twitter ya dakatar da shafin babban ɗan shugaban ƙasar Amurka wato Donald Trump.

Jam’iyya mai mulki a ƙasar Uganda ta tsayar da Yoweri Museveni amatsayin ɗan takarar zabe a shekarar 2021.

Ma’aikatar harkokin wajen Jamus ta gargaɗi ‘yan ƙasar game da yin balaguro zuwa yankuna uku na kasar Andalus saboda wasu manyan dalilai.

Daga bangaren wasanni kuwa:

 

Ayau gidan rediyon Aminchi ya karɓi baƙuncin shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta jahar Kano kuma wakili a hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa sannan shugaban kwamatin naɗa alƙalan wasa wato Dr. Sharu Rabiu Inuwa Ahlan.

Ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid wato Mariano Diaz ya kamu da cutar Coronavirus.

An bayyana kuɗaɗen daza a rabawa ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasarnan dasuke buga gasar ajin Firimiya domin rage raɗaɗin cutar Coronavirus.

Comments
Loading...