Mai Horas da Rarara Yace Sunshirya Tsaf Awasansu da Sokoto

22

Daga Suraj Na’iya Kududdufawa.

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Rarara wato Bashir Adede dake buga wasanta a filin wasa na Rara dake garin Kahutun jahar Katsina ya bayyana cewa sun shirya tsaf domin buga wasan mako na biyu na gasar ajin kwararru ta kasar nan.

Mai horas war ya bayyanawa gidan rediyon Aminchi dake jahar Kano hakanne daga can jahar Sokoto inda zasu buga wasa da Sokoto.

Kungiyar kwallon kafan ta Rara ta buga kunnen doki awasan mako na 1 inda yanzu suke da maki 1.

Haka mai horas war ya kara da cewa kungiyar tasu ta tanaji kwararrun ‘yan wasa inda ayanzu zata iya tunkarar kowacce kungiya ga misali nan na abin da kungiyar tayi a gasar share fage ta Ahlan.

Duk da kungiyar tasu ta rabu da wasu manyan ‘yan wasa inda wani ya tafi Katsina United wani kuma ya tafi Plateau United da sauransu to amma yanzu sun mai da gurbin wadancan.

Daga karshe yayi addu’ar fatan cewa kungiyar ta sami tikitin buga gasar ajin Premier ta kasar nan.

Comments
Loading...