NAJERIYA ZATA NEMI HADIN KAN AMURKA DANGANE DA KUDIN SATA

7

Yanzu haka dai Ministan Shari’ar kasar nan Abubakar Malami, na halartar wani taron hadin gwiwa na kwana uku tsakanin Najeriya da Amurka a birnin Washington, inda zai rattaba hannu kan wata yarjejeniya game da kudin gwamnatin da aka sace a kasar nan.

A madadin gwamnatin tarayya, ana sa ran ministan zai saka hannu kan wata yarjejeniya da yankin Island of New Jersey da kuma kasar Amurka kan kudaden sata da aka kai Amurka aka boye, daga Najeriya.

Kudin da aka sace sun kai dalar Amurka miliyan 321 dai dai da naira Biliyan 116 a yunkurin gwamnatin Shugaba Buhari na dawo da kudaden da aka sace zuwa lalitar Najeriya.

 

Comments
Loading...