Ayau za a fafata wasan karshe na gasar Super Cup tsakanin manyan kungiyoyin kwallon kafa guda biyu kuma wadanda suka fito daga birni daya wato birnin Madrid na kasar Andalos.

Wannan wasa za ayishi tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da Athletico Madrid.

Inda za a fafata wannan wasa a kasar Saudiyya da misalin karfe 7:00 na dare agogon Najeriya.

Acikin shekaru 6 dai kungiyoyin kwallon kafan guda biyu sun fafata wasannin karshe sau 3 inda suka fafata guda biyu agasar zakarun nahiyar turai a 2014 da 2016 inda Real Madrid ta lashe Athletico Madrid aduk wasanni biyun.

Sai kuma a gasar Toyota inda Athletico Madrid ta lashe Real Madrid.

Shin ko yau waye zai zamo zakara?

Sashen wasanni na Aminchi Radio ya tattauna ya tattauna da Aliyu Safyan Alhasan wanda magoyin bayan Real Madrid ne dake jahar Kano kuma daya daga cikin ma’aikatan Aminchi Radio na sashen siyasa inda yace “mu Real Madrid duniya ne kuma ni naso ace Barcelona ne suka fito wasan karshen nan aga yadda zamu ragargazasu domin sai sunfi saukin cinyewa, amma duk da haka suma Athletico Madrid insha Allah zamu lashesu daci 2 da 1 domin wasan kariya zasuyi wato defending”

Make Comment

Comment