Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunan sabon shugaban hukumar alhazai ta kasa da mambobinta ga majalisar dattijai domin tantancewa.

Majalisar dattawan da kanta ta wallafa a shafinta na Twitter cewa ta karba gami da bitar wata wasika da Shugaban ya aiko zauren dangane da nada sabon Shugaban Hukumar.

Sai dai majalisar ba ta yi karin bayani kan ko waye sabon shugaban Hukumar Alhazan ta kasa da shugaban ke son nadawa ba, wanda yanzu haka Abdullahi Mukhtar dan asalin jihr kaduna ke shugabantar hukumar mai ci a halin yanzu.

Make Comment

Comment