Posts

Yau Laraba 11/03/2020CE – 16/07/1441AH.

Ga cikakken labaran:

Gwamna El-Rufa’i na jihar Kaduna ya nada Muhammadu Sunusi II a matsayin Chancellor na Jami’ar jihar Kaduna.

Rundunar ‘yansanda ta kama wasu kansilolin Zamfara da laifin garkuwa da mutane.

Gwamnatin Najeriya ta karbo kudin sata N3b daga hannun ‘Yan kwangila a Neja-Delta.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce bullar Coronavirus ya janyo kudaden shiga da Najeriya ke samu daga bangaren man fetur ya ragu.

Majalisar dattawa ta gabatar da kudurin da zai hana amfani da injin janareto a Najeriya.

‘Yan bindiga sun sace ‘yan bautar kasa guda hudu a jihar Katsina.

Daya daga cikin matan Sanusi II da yaranta 3 sun isa gidansa na garin Awe da rakiyan jami’an DSS.

Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari ya ce a shirya shiga matsanancin hali a Najeriya.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta ce kashi 60 zuwa 70 na jama’ar kasar na iya kamuwa da cutar corona.

Shugaba Trump na Amurka ya karyata rahoton cewa ya kamu da cutar Coronavirus.

Wasu gungun mutane kusan 100 a Moscow suna zanga-zangar adawa da yunkurin sake tsayawa takarar Putin.

Yau 22/05/1441AH wanda yayi daidai da 18/01/2020CE

Kiris yarage asha bikin wata baturiya datazo daga kasar Amurka da saurayin dazata aura dan asalin jahar Kano wanda suka hadu a dandalin sada zumunta.

Gawurtaccen mai garkuwa da mutane, Buju Bazamfare ya mika kansa ga hukuma a jihar Nasarawa.

Jagorar IPOB, Nnamdi Kanu zai shigo Najeriya jana’izar iyayensa wata mai zuwa.

Shugaban sojojin sama, AM Saddique ya ce an sayi jiragen yaki don kawar da Boko Haram.

Badakalar satar N200m: jami’an EFCC sun kama akawun majalisa, matarsa da yaransa 2 a jihar Benue.

Tanko Yakasai ya ce dole ne Inyamurai su hada kai da mutanen Arewa muddin suna son su mulki Najeriya.

Shugaban sojoji, Buratai ya amincewa sojoji amfani da sigari da sauran abubuwan more rayuwa a fagen fama.

Jam’iyyar PDP za ta shirya zanga-zanga kan hukuncin da kotun koli ta yanke na gwamnan jihar Imo.

Sudan ta kudu ta gaza kulla yarjejeniyar sulhu da ‘yan tawaye.

lsraila ta kame wasu ‘yan kasar Finlan su 5 a yayin da suke kan hanyarsu ta shiga Zirrin Gaza daga yankin Israila.

Indiya ta samu nasarar harba tauraron dan adam na GSAT-30 zuwa duniyar sama.

Masu horas wa sama da 50 ne suka nuna sha awarsu ta horas da kungiyoyin kwallon kafa na kasar nan kama daga ‘yan kasa da shekara 17 zuwa Super Eagles.

Harry Maguire ya zama sabon Kaftin din kungiyar Manchester United.