Takaitattun Labaran Yammacin Litinin

3

Yau 02/12/2019CE Wanda yayi daidai da 05/04/1441AH.

Shugaba Buhari ya aikewa majalisa da bukatar gabatar da takardun biyan haraji kafin bude asusun ajiya a banki.

Babbar kotun tarayya ta yi watsi da karar da hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta shigar a kan kalubalantar sifeta janar, na diban ma’aikata 10,000 da ya yi.

An gano furofesoshi sama da guda 100 na bogi a nan Nigeria.

Gwamna Ganduje na jihar Kano ya sake gabatar da kudirin kafa sabbin masarautu 4 ga majalisar jihar.

Shugaba Buhari ya kaddamar da fara ginin sabuwar jami’ar koyar da ilimin Sufuri a mahaifarsa da ke Daura, jihar Katsina.

Tsohon shugaban kasa, Jonathan ya ce ‘yan siyasar Afrika sun dawo da salon juyin mulkin farar hula.

Gwamna Nasir El-Rufai ya rattafa hannu kan kasafin kudin shekarra 2020 na jahar Kaduna da ya kai naira biliyan 259.25.

Katsina: Wani matashi mai suna Yusuf Lawal ya halaka wani dansanda mai suna Kofur Musa Isiyaku da almakashi.

Rufe boda: Ministan yada labarai, Lai Muhammad ya ce ana samun ci gaba a fannin kasuwanci da noma.

Wani dan majalisar wakilan tarayya daga jihar Neja, Jafaru Iliyasu Auna, ya rigamu gidan gaskiya.

Mutane 3 sun rasa rayukansu sakamakon fadowar wani karamin jirign sama a jihar Texas dake Amurka.

Jami’an tsaro 2 sun rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai musu a Kabul Babban Birnin Afganistan.

Daga fagen wasanni kuwa kungiyar kwallon kafa ta Jigawa Golden Star ta lallasa Ifenyi Uba ayammacin yau Litinin daci 2 da 1.

Comments
Loading...