Wasu Daga Cikin Labaran Safiyar Alhamis

18

Yau Alhamis 26/03/2020CE wanda yayi daidai da 01/08/1441AH.

Ga Cikakkun labaran:

Shugaba Buhari ya koma bakin aiki bayan zaman dar-dar din shigar Covid-19 Villa.

Ya zuwa yanzu jimillar masu dauke da kwayar cutar COVID-19 a Najeriya ya koma mutum 51 a jihohi 9.

Gwamnatin jihar Kaduna ta haramta amfani da a-daidaita-sahu da motocin taxi a jihar don kaucewa yaduwar cutar Coronavirus.

‘Yanbindiga sun kashe mutane 29 a jihar Neja.

Sakamakon gwajin Coronavirus da aka yi ma gwamnan Nassarawa ya nuna cewa ba ya dauke da cutar.

Coronavirus: Kamfanonin jiragen Air Peace da Dana sun dakatar da ayyukansu.

An yi garkuwa da dan uwam gwamnan Bauchi kwana daya da kamuwarsa da Coronavirus.

Dangote ya shawarci gwamnati ta kyale asibitoci masu zaman kansu gwajin citar Covid-19.

Coronavirus: Gwamnan jahar Ondo ya killace kansa bayan mu’amala da gwamnan Bauchi.

Gwamna Diri na jihar Bayelsa ya musanta cewa ya hadu da Abba Kyari ko Muhammed Atiku.

Kasar Amurka za ta binciki gwamnatin China game da sakaci kan Coronavirus.

Gwamnatin kasar Africa ta Kudu ta haramtawa masu gidajen haya karbar kudin haya na tsawon watanni 3 saboda Coronavirus.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta shiga neman dan wasan gaban Brussia Dortmund wato Erlin Braut Haaland.

Shahararren dan wasan Tenis wato Roger Federer da matarsa sun bayar da gudun mawar kudi masu yawa ga ‘yan kasar Switzerland saboda cutar Coronavirus.

Comments
Loading...