Ana zargin wani magidanci da karbar Naira dubu 50 daga wadanda ake zargi da yi wa ‘yarsa ciki a jihar Sakkwato.

Wadanda ake zargi da wannan aika aika dai sun hadar da Daraktan Kudi na jihar ta sokoto Ahmad Yahaya Nawawi, da Habibu Abubakar da kuma Karin wani mutum guda da dukkansu ke aiki a Hukumar Tsara Birane bayan da suka yi watanda da yarinyar ‘yar shekaru 14 a duniya mai sayar da ruwan leda, a ofishin daya daga cikinsu abin da ya haifar da shigar cikin da a yanzu ya kai watanni shida.

Sai dai tuni wadanda ake zargi suka amsa laifinsu a ofishin Hukumar dake yaki da masu safarar Mutane ta kasa wato NAPTIP.

Sai dai da yake bawa da bakinsa wuyar sayarwa ne da shi, daya daga cikin wadanda ake tuhumar Nawawi, ya shaida cewa kage ne kawai aka kitsa musu mai cike da siyasa don a bata masa suna a jihar.

 

Make Comment

Comment