YADDA BUKIN YAN MATANCI A KASAR JAPAN YAKASANCE—HOTU NA

8

Kasar Japan ta bayyana ranar ‘yan matanci a kasar, inda akan bai wa dalibai da ma’aikata hutu dan taya ‘yan matan da suka kai shekara 20 murna, kuma ana gudanar da bikin ne a hukumance dan yi musu maraba da kai wa wannan lokacin.

Ana gudanar da wannan biki ne a ranar Litinin ta biyu a watan Janairun kowacce shekara, ‘yan matan da suka cika shekara 20 a shekarar da ta gabata ake sanya wa a bikin da ake yi a wani babban dakin taro da ke birnin Tokyo da sauran wurare a kasar.

Wannna biki dai dadaddiyar al’ada ce da aka fara samar da ita a shekarar 1876, to amma a shekarar 2018 gwamnatin Japan ta ayyana ta a matsayin doka tare da rage shekarun budurcin daga 20 zuwa 18 don haka biki na gaba da za a yi shi ne a shekarar 2022.

 

 

Comments
Loading...