YAN ISRAILA ZASU FARA ZUWA MAKKAH A KARON FARKO

5

Ministan cikin gida na kasar Isra`ila Aryeh Deri ya bayyana cewa  a yanzu, inda yace Isra’ilawa mabiya addinin musulunci suna da damar yin balaguro zuwa saudiyyar ko dai tafiyar kasuwanci ta kwanaki 9, ko kuma gudanar da ayyukan ibada kamar yadda suka so.

Sai dai kawo yanzu hukumomin Saudiyyar ba su fitar da sanarwa kan batun a hukumance.

A baya dai kasashen Isra’ila da Saudiyya ba su da wata cikakkiyar alakar diplomasiyya tsakaninsu, sai dai a baya-bayan nan wasu rahotannin sirri na bayyana cewa kasashen biyu na kokarin sasantawa dan yakar kasar Iran da suke yi wa kallon makiyarsu.

Kasar Isra’ila dai ta sanar da cewa za ta amince ‘yan kasar su je Saudiyya a karon farko, a wani yunkuri da ake ganin na yaukaka dangantaka ne tsakanin kasashen biyu, duk da wasu na ganin alakar ta baka na baka ne.

 

 

Comments
Loading...