Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana cewar wasu mutane ne yan kalilan ke gayyato masu satar mutane jihar domin biyan bukatar kansu da kansu.

Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa mazauna garuruwan da ke kan iyakar Najeriya da Nijer ne suka fi yin wannan ta’ada musamman mutanen garin Jibiya.

Ko a ranar Alhamis sai da gwamnan a cikin wani bidiyo wanda yake ta karakaina a shafukan sada zumunta, ba tare da kumbiya-kumbiya ba ya kama sunan mutanen Jibiya inda ya ce su ne ke kara lalata harkar tsaron garunsu da kansu.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wasu jami’an kwastam guda biyu a wani shinge da ke kauyen Dan-bedi a yankin karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina mai iyaka da jamhuriyar Nijer.

Batun hare-hare da sace jama’a dai ya zama ruwan dare a jihar Katisna, inda da wuya rana ta fito ta fadi ba tare da samun wani gari ko kauyen da aka masu satar jama’a suka far wa ba.

Make Comment

Comment