‘Yan Wasan Da Sukafi Samun Katin Gargaɗi Agasar Laliga Da Aka Kammala

120

Bayan kammala gasar Laliga ta ƙasar Andalus da akayi a ƙarshen makon daya gabata inda aka buga wasanni guda 380 bayan kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta buga wasanni guda 38.

Ayanzu ansami jerin ‘yan wasan dasukafi karɓar katin gargaɗi wato yellow card daga ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa daban-daban:

Ga jerin sunayen’yan wasan da adadin yadda kowannensu ya karɓa:

1. Suarex na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Getafe ya karɓa sau 15.

2. Gerrad Pique na Barcalona ya karɓa sau 15 shima.

3. Soldado na Granada ya karɓa sau 14.

4. Mata na Getafe shima ya karɓa sau 14.

5. Herrera na Granada shima ya karɓa sau 14.

6. Oier na Granada ya karɓa sau 14.

7. Nyom na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Getafe ya karɓa sau 13.

8. Silva na Leganes ya karɓa sau 13.

9. Thomas Partey na Athletico Madrid ya karɓa sau 13.

10. Fernando na Sevilla ya karɓa sau 13.

Comments
Loading...