Daga Suraj Na’iya Kududdufawa.

Wani mutum mai suna Jumare Bulama ya rabu da matarsa akan ta kushe shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Dabai ta jahar Katsina dake Arewa maso Yammacin Najeriya.

Dattijon daman tuni yake ikirarin cewa shifa zai iya rabuwa da kowa akan Buhari.

Matar tasa mai suna Hajara Abdullahi Giwa ta bayyana cewar sama da shekara 30 babu wani abu daya taba hadasu da mijinta amma kwatsam akan ta kushe Buhari ya sallameta.

Amma daga bisani mijin matar ya bayyana cewar tunda dai ba saki uku yayiwa matarsa ba to ashirye yake ta dawo su dora a zaman aurensu amma saita kiyaye harshenta wajen sukar Buhari.

Make Comment

Comment