Yau Za’a Baiya Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Liverpool Kofin Firiya

35

Tabbas dukkanin abin da aka sanyawa rana zaizo domin kuwa ranar da aka bayyana cewar za a baiwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool gasar ajin Firimiyar Ingila tazo wato ranar 22 ga watan Yuli na shekarar 2020.

Liverpool dai ta lashe gasar ta Firimiya da tazarar maki mai yawa data baiwa ƙungiyar datake biye da ita wato ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City, saidai Liverpool tun bayan dayarage saura wasanni bakwai a kammala gasar ƙungiyar ta zamo zakara.

Adaren yau dai bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool da Chelsea sun tashi awasan mako na 36 za abasu gasar da suka lashe, Liverpool dai rabon datalashe gasar kimanin shekaru 30 inda sai awannan shekarar suka lashe.

Daga wasanni 36 da ƙungiyar ta Liverpool ta fafata ta lashe wasanni guda 30 sannan ta buga kunnen doki awasa 3, haka zalika tayi rashin nasara awasanni guda 3, ta jefa ƙwallaye guda 77 yayin da akajefamata 29.

Comments
Loading...